Mutane sun bar gidajensu don ambaliyar ruwa da ta lalata garuruwa 10 a Kebbi – NEMA
Mutane sun bar gidajensu don ambaliyar ruwa da ta lalata garuruwa 10 a Kebbi – NEMA
Ambaliyar ruwa
Daga Ibrahim Bello
Shanga (Jihar Kebbi), Satumba 25, 2024 (NAN) Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta ce al’ummomi goma ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a karamar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi.
Mista Aliyu Shehu-Kafindagi, shugaban hukumar NEMA a Sokoto ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagar hadin guiwa zuwa yankunan da abin ya shafa a ranar Laraba.
Ya kara da cewa lamarin ya bar mutane akalla 2,000 da suka rasa matsugunansu, wadanda ba su da wani zabi da ya wuce guduwa zuwa wasu wuraren.
“Al’amarin da ya faru a tsakanin 17 zuwa 22 ga watan Satumba, a sakamakon ruwan sama mai yawa ne da kuma samun karin ruwa daga kogin Neja, lamarin da ya sa wasu ginegine suka nutse.
“ Garuruwa 10 da abin ya shafa a karamar hukumar Shanga, sun hada da, Kunda, Dala- Maidawa, Dala-Tudu, Dala-Mairuwa, Ishe-Mairuwa, Kwarkusa, Kurmudi, Tugar Maigani, Tukur Cika, Uguwar Gwada, Uguwar Wakili da Gundu, ” in ji shi.
A cewarsa, mutanen da suka rasa matsugunansu, galibi masunta ne, wadanda suka yi hasarar kadada mai yawa na gonaki.
Ya ce dukkanin amfanin gonakinsu iri-iri da suka hada da shinkafa, masara, gero, wake, da masara da dai sauransu sun nutse a cikin ruwa.
Shugaban hukumar ta NEMA ya kuma bayyana cewa, a yayin da tawagar ta gudanar da tantancewar, ta gano sansanin ‘yan gudun hijira da ke makarantar firamare ta Tudun Faila, inda sama da mutane 300 suka samu mafaka.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, an gudanar da atisayen tantancewar hadin gwiwa da hukumar NEMA ta yi ne tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA, da jami’an karamar hukumar Shanga, da kuma jami’an tsaro a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
IBI/KLM
======
Muhammad Lawal ne ya gyara