Mutane 25 sun mutu, 14 sun bace a hatsarin jirgin ruwa a Yobe

Mutane 25 sun mutu, 14 sun bace a hatsarin jirgin ruwa a Yobe

Spread the love

Hadari

Nabilu Balarabe

Damaturu, Janairu 5, 2026 (NAN) Akalla mutane 25 ne suka mutu yayin da wasu 14 suka bace bayan kifewar wani kwale-kwale a bakin kogin Yobe a garin Garbi, karamar hukumar guru ta jihar.

Dakta Mohammad Goje, Sakataren zartarwa na hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA), ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:48 na yamma a ranar 3 ga Janairu, bayan da wadanda abin ya shafa, wadanda galibi manoma ne da ‘yan kasuwa, suka shiga jirgin ruwa a garin Adiyani da ke makwabtaka da Jigawa.

Goje ya ce, “An ruwaito cewa wadanda abin ya shafa, suna dawowa ne daga garin Adiyani, inda suke aikin kamun kifi, noma, da sauran harkokin kasuwanci na gida, lokacin da kwale-kwalen ya kife a tsakiyar tafiya.”

Sakataren zartarwar ya kara da cewa an ceto fasinjoji 13 daga bala’in, kuma suna karɓar magani a asibiti.

“Ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto, inda hukumomin tsaro, masu ba da agajin gaggawa, da kuma masu aikin sa kai na al’umma ke aiki don gano fasinjojin da suka ɓace da kuma gano gawarwakinsu.”

“Tun daga lokacin aka tura tawagar bincike da ceto ta SEMA, daga Bade da Nguru, don tallafawa tawagar da ke ƙasa,” in ji shi.

Goje ya ce, Gwamna Mai Mala Buni ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, sannan ya umurci YOSEMA da ta samar da tallafin lafiya da kayan aiki ga wadanda aka ceto.

Sakataren zartarwar ya tabbatar cewa, gwamnan ya jaddada cewa dole ne a hanzarta ayyukan tura mutane domin ceto rayuka ba tare da ɓata lokaci ba.(NAN)(www.nannews.ng)

NB/YMU

An gyara ta Yakubu Uba

Fassarar Aisha Ahmed

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *