Miji na yana bani Naira 50 ne kawai na abinci, wata mata ta shaida wa kotu

Miji na yana bani Naira 50 ne kawai na abinci, wata mata ta shaida wa kotu

Spread the love

Miji na yana bani Naira 50 ne kawai na abinci, wata mata ta shaida wa kotu

Abinci
Daga Aisha Gambo
Kaduna, Agusta 9, 2025 (NAN) Wa
ta mata mai suna Hauwa’u Bello da ke fama da matsalar ji, ta maka mijinta, Usman Shuaibu a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin cikin birnin Kaduna.

Ta ce mijin yana bata Naira 50 kacal domin abinci.

Mai shigar da karar wadda ta yi magana ta hanyar yaren kurame, Aisha Sulaiman, ta fassara ta ce mijin nata yana fama da yunwa.

Ta ce “mun yi aure a shekarar 2016, iyayena sun ba mu abinci, matsalar ta fara ne bayan kayan abincin ya kare.

Ya gaza wajen samar da gida, tela ne.

“Lokacin da na haifi jariri na, ya kasa biyan kudin asibiti, mahaifiyarsa ce ta ba da kudin,” in ji ta.

Ta ce iyayensu sun shiga tsakani kuma sun shawarci mijinta ya biya bukatun iyalinsa, amma bai canza ba, sai ta roki
kotu da ta raba auren.

Amma kuma, Shuaibu ya musanta ikirarin, inda Alkalin kotun, Malam Kabir Muhammad, ya umarci ma’auratan da
su gabatar da iyayensu ko masu kula da su a ranar 25 ga watan Agusta saboda cigaba ga karar.(NAN) (www.nannews.ng)

AMG/HA

=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta gyara

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *