Masu ruwa da tsaki sun ba da shawarar aiki da dabarun haɓaka noman zamani
Masu ruwa da tsaki sun ba da shawarar aiki da dabarun haɓaka noman zamani
Dabarun
By Doris Isa
Abuja, Satumba 19, 2024 (NAN) Kungiyar Organic and Agroecology Initiative (ORAIN), tare da hadin gwiwar gidauniyar Heinrich Boll, ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su yi amfani da dabarun noma domin bunkasa ayyukan samar da abunci.
Mista Ikenna Ofoegbu, jami’in kula da ayyuka na gidauniyar Heinrich Boll ne ya yi wannan kiran a taron masu ruwa da tsaki na kasa kan habbaka noman zamani a Najeriya a aka yi ranar Alhamis a Abuja.
Ofoegbu ya ce hakan na daga cikin shawarwarin taron bitar da aka gudanar a watan Yuni.
Agroecology wani aikin noma ne mai dorewa wanda ke aiki tare da yanayi. Yana da aikace-aikacen amfani da yanayin muhalli da ka’idojin noma.
Ofoegbu ya ce dabarun aikin gona na kasa na neman tsarawa tare da aiwatar da cikakken dabarun da suka dace da manufofin samar da abinci da hada kai a sassa daban-daban don inganta ayyukan noma mai dorewa.
Ya ce wasu shawarwarin sun hada da kara kudade don ayyukan noma, zayyana takamaiman wurare don noman ire-ire na musassaman da kare su daga gurbatar masana’antu da ayyukan da suka shafi al’adu.
Sauran sun kasance tallafin shirye-shiryen horarwa don ilimantar da manoma kan ayyukan noma, noman kwayoyin halitta da dabarun noma mai dorewa.
Masu ruwa da tsakin sun yi kira ga majalisun tarayya da na jihohi da su samar da dokoki masu taimaka wa ilimin aikin gona.
Sun yi kira ga gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu da su samar da lamuni ga masu karamin karfi da kuma karfafa hanyoyin noman ire-ire na musassaman.
Hadaddiyar kungiyar ta bukaci kungiyoyin manoma da kungiyoyin hadin gwiwa da su rungumi ayyukan noma tare da saukaka hanyoyin samun kasuwa don samar da kayayyakin amfanin gona da sauransu. (NAN) (www.nannews.ng)
ORD/KAE
=====
Kadiri Abdulrahman ne ya gyara shi