Masani ya yi gargadi game da shan ruwan kwalba da aka bari a rana

Masani ya yi gargadi game da shan ruwan kwalba da aka bari a rana

Spread the love

Masani ya yi gargadi game da shan ruwan kwalba da aka bari a rana

Gargadi
Daga Fatima Mohammed-Lawal
Ilorin, Feb. 19, 2025 (NAN) Farfesa Uthman Mubashir, kwararre a fannin Kiwon Lafiyar Jama’a da Magunguna
na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH), ya gargadi mutane game da shan ruwan kwalba da abubuwan sha da
aka bari a rana.

Mubashir, a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Ilorin, ya ce ya kamata a
guje wa ruwan da ke cikin kwalbar robobi da aka bari
a karkashin zafin rana na kimanin digiri 45.

NAN ta lura cewa abu ne da aka saba gani a shaguna da rumfunan da ke fadin birnin Ilorin don ganin fakitin ruwan
kwalba, kayan shaye-shaye da kuma sanannen “pure water” da ke cikin leda, wanda aka bar shi a karkashin rana
ana sayarwa.

Da yake bayani kan wannan al’ada, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken kimiyya wanda ya jaddada cewa kayan
kwalaben robobi na iya zama sanadin kamuwa da cutar daji.

Mubashir ya gargadi mutane da su guji barin ruwa ko abin sha a cikin kwalabe na roba a wajen rana ko yanayin zafi.

Ya ce barin ruwa a cikin kwalabe na robobi a cikin zafin rana na iya zama hadari, domin zafi na iya sa sinadarai daga robobin su shiga cikin ruwa, wanda hakan zai iya zama illa ga wadanda suka sha, har su kamu da cuta.

Don haka masanin ya shawarci ‘yan Najeriya da su rika shan ruwan ma’adinai mai tsafta akai-akai, saboda zafi da kuma gujewa kamuwa da tsananin zafi. (NAN)(www.nannews.ng)
FATY/FON/HA
============
Florence Onuegbu da Hadiza Mohammed-Aliyu ne suka gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *