Manyan mutane sun halarci jana’izar Buhari, sun yi masa fatan alheri a Daura
Manyan mutane sun halarci jana’izar Buhari, sun yi masa fatan alheri a Daura
To masu fatan alheri
Daga Abbas Bamalli
Daura (Katsina), Yuli 15, 2025 (NAN) Dubban masoya da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Sarakunan Zazzau, Kazaure, Dutse da Sarkin Kano na 19, suna Daura, Katsina, sun halarci birne gawar tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, gawar tsohon shugaban kasar da ya rasu ranar Lahadi a birnin Landan ta samu tarba daga shugaban kasa Bola Tinubu a Katsina.
Gawar ta taso ne daga filin jirgin Katsina zuwa Daura, mahaifar sa, a cikin ayarin motoci tare da rakiyar Tinubu da manyan jami’an gwamnati
Ana sa ran za a amsar gawar Buhari a garin Daura bayan an idar da sallah.
Sauran jiga-jigan sun hada tsohon shugaban kasa, Gwamnan Bauchi, Alhaji Bala Mohammed, da tsaffin gwamnonin Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Sokoto, Aminu Tambuwal.
Sauran sun hada da tsoffin gwamnonin Kogi, Yahaya Bello; Borno, Alimodu Sherif; Ekiti, Kayode Fayemi; Katsina, Aminu Masari, Kebbi, Adamu Aliero.
Sauran sun hada da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, tsohon gwamnan Kebbi, Adamu Aleru, tsohon IG na ‘yan sanda Adamu, Amb. Babagana Kigebe,
NAN ta kuma ruwaito cewa, wasu dubban masu fatan alheri ne suka hallara a wurin taron domin yiwa tsohon shugaban kasar bankwana, inda za a yi sallar jana’izar a Daura. (NAN) ( www.nannews.ng )
AABS/ROT
========
Rotimi Ijikanmi ne ya gyara shi