Mamakon ruwan sama yana yi mana barazana – manoman shinkafa a Abakaliki
Douglas Okoro
Abakaliki, 6 ga Agusta, 2025 (NAN) Manoman shinkafa a Abakaliki, sun koka kan yadda ake samun mamakon ruwan sama, wanda a cewarsu yana barazana ga noman shinkafa a shekarar 2025.
Manoman, sun bayyana damuwar tasu ne a wata tattaunawa da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba a garin Abakaliki.
An dai samu mamakon ruwan sama a bana wanda ya yi sanadin ambaliya da asarar amfanin gona a manyan yankunan da ake noman shinkafa a jihar.
Mista Emmanuel Nwali, wani fitaccen manomin shinkafa a karamar hukumar Izzi, ya ce kusan rabin gonar shinkafarsa ta nutse sakamakon ruwan sama mai yawa.
“Ambaliya ta lalata yawancin gonakinmu, abin da ya rage tuni ya koma tawaya.
“Kusan kullum ana ruwan sama tun tsakiyar watan Yuli. Wataƙila ba za mu yi tsammanin samun girbi mai yawa a wannan kakar ba,” in ji Nwali.
Wani manomi, Mista Chinedu Okenwa, ya ce ya yi asarar gidajen yara na reno sakamakon ambaliyar ruwa, wanda ya yi sanadin asarar manyan albarkatu.
“Ban san yadda zan gyara asarar da aka yi ba, domin a halin yanzu, ba zan iya dasa komai ba don ya lalace.
“Muna fuskantar karancin amfanin gona a wannan kakar, kuma hakan na iya haifar da hauhawar farashin shinkafar gida a shekara mai zuwa,” in ji shi.
Hakazalika, Mista Aloysius Njoku, wani Mai nomana kasuwanci, ya ce ya yi asarar wani kaso mai yawa na gonar shinkafa sakamakon ambaliya, kuma yana fargabar ci gaban zai yi illa ga girbi.
“Damina da ambaliyar ruwa sun yi mummunar barna, idan ba a yi wani abu ba, shinkafa za ta yi karanci da tsada, kuma kowa zai ji ajikinsa,” in ji Njoku.
Misis Sylvia Elom, wata ma’aikaciyar gwamnati kuma mai noman shinkafa, ta bayyana ddamuwarta inda tace barnar da ruwan sama ya yi a gonaki ta yi kamari kuma abun zai shafi mutane da dama da suka dogara da noman shinkafa domin tafiyar da rayuwarsu.
“Shinkafa ita ce babbar hanyar samun kudin shiga ga yawancin mutanenmu wadanda galibi manoma ne, idan ambaliyar ruwa ta lalata mana gonakinmu, ba a bar mu da komai ba kenan,” in ji ta.
A halin da ake ciki, Dr Paul Onwe, wani kwararren manoma mai zaman kansa, ya bayyana cewa akwai gagarumar matsala a noman shinkafa idan damuna ta tsawaita aka samu ambaliya.
Ya kara da cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya, yana haifar da babbar barazana ga gonakin shinkafa, musamman wadanda ke cikin fadamu.
Ya shawarci manoma da su mai da hankali sosai kan hasashen yanayi kafin su fara noman shinkafa, yana mai cewa gwamnatin tarayya na bayar da gargadin a farkon kowace kakar noma.
“Filayen da ke cikin ƙasa suna fama da takurewar girma, ƙarancin abinci mai gina jiki, da cututtukan fungal,” Onwe yayi gargaɗi.
Wata majiya daga ma’aikatar noma ta jihar Ebonyi da ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar na bin diddigin illolin da ambaliyar ruwa ta haifar a gonaki a halin yanzu.
Ya kara da cewa gwamnati na kuma tattara rahotanni daga yankunan da abin ya shafa domin daukar matakan da suka dace.
NAN ta ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), a hasashenta na yanayi, ta bayyana jihar Ebonyi a matsayin daya daga cikin jihohin da ake sa ran za su fuskanci ambaliyar ruwa a lokacin damuna ta 2025.
Jihar Ebonyi dai na daya daga cikin jihohin da ake noman shinkafa a Najeriya, kuma ‘yan kasuwar shinkafa a manyan kasuwannin Abakaliki, sun bayyana fargabar cewa farashin shinkafar na iya tashi sakamakon rashin girbi da ake sa ran za a samu. (NAN) (www.nannews.ng)
Edited by Aisha Ahmed