Makaho yakai masoyiyarshi kotu don kin aurensa
Makaho
Daga Aisha Gambo
Kaduna, Feb. 25, 2025 (NAN) A ranar Talata ne wani mutum mai nakasa mai suna Kurma Haruna ya kai wata masoyiyarsa mai suna Malama Bilkisu gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari a jihar Kaduna saboda ta ki aurensa.
Wanda ya shigar da karar, mazaunin unguwar Hayin Dan-mani, ya kuma roki kotun da ta taimaka masa ta kwato masa asusun ajiyarsa na kudi
N100,00 daga hannun wanda ake kara.
Alkalin kotun, Malam Kabir Muhammad, ya bukaci mai karar da ya gabatar da shaidu inda ya gabatar da dan uwansa Abubakar Haruna.
Dan’uwan ya bayyana cewa Haruna ya dade yana ajiye kudinsa tare da wanda ake kara, inda ya kara da cewa matsala ta fara ne lokacin da ya
nemi kudinsa.
Yace “kurma Haruna ya kasance yana ba ta (Malama Bilkisu) Naira 2,000 zuwa Naira 5,000 domin ajiyewa idan ya bukaci kudi, har ya
lissafta adadin da ya ajiye ya kai Naira 175,000.
“Da kurma Haruna ya tambayi wacce ake tuhuma kudinsa, sai tace Naira 80,000 kawai za ta iya tunawa, al’amarin da ya sanya suka garzaya
kotun shari’a a Rigasa, Kaduna.
“Ta gabatar da Naira 80,000 a gaban kotu amma kurma ya ki karbar kudin, yana mai cewa bai gamsu ba.”
A cewar mai shaida, alkalin lokacin ya bayyana cewa bangarorin biyu za su rantse da Alkur’ani mai girma, amma sun ki komawa kotun tun
daga lokacin.
Daga bisani, sai Malam Kabir Muhammad, alkalin kotun shari’a da ke Magajin Gari a jihar Kaduna ya dage sauraron karar zuwa ranar 17
ga watan Maris, domin lauyan wanda ake kara ta gabatar da adireshinta. (NAN)
AMG/IFY
=========
Ifeyinwa Omowole ce ya gyara