Majalisar dattawa ta tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin ministan tsaro
Majalisar dattawa ta tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin ministan tsaro
Tabbatarwa
Daga Naomi Sharang
Abuja, Dec. 3, 2025 (NAN) Majalisar dattawa ta tabbatar da tsohon shugaban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin ministan tsaro.
- Majalisar Dattawa ta tabbatar da Musa a ranar Laraba ta hanyar kada kuri’a bayan an shafe sa’o’i ana tantancewa a cikin kwamitin baki daya, inda ‘yan majalisar suka yi masa tambayoyi da dama.
Musa, wanda ya yi murabus kwanaki 40 da suka wuce, Shugaba Bola Tinubu ne ya nada shi a matsayin Ministan Tsaro a ranar Talata kuma ya mika wa majalisar dattawan don tabbatar da shi.
Cikakken bayani zai zo nan gaba. (NAN) (www.nannews.ng)
NNL/BRM
=========
Edited by Bashir Rabe Mani

