Majalisar dattawa ta amince da kudirin kafa hukumar raya Kudu maso Yamma
Majalisar dattawa ta amince da kudirin kafa hukumar raya Kudu maso Yamma
Kuduri
By Kingsley Okoye
Abuja, Satumba 26, 2024 (NAN) Majalisar dattawa a ranar Alhamis a zamanta ta zartas da kudirin neman kafa hukumar raya Kudu maso Yamma.
Amincewar kudirin ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin ayyuka na musamman da shugaban majalisar Sen. Kaka Shehu (APC-Borno) ya gabatar.
Shehu, a cikin jawabinsa ya ce an tsara kudirin ne don ciyar da zamantakewar al’umma – bunkasar tattalin arzikin Kudu maso Yamma.
“Idan an kafa hukumar ta hanyar amincewar shugaban kasa kan kudirin, za ta kawo ci gaba da Kuma kwamitocin da aka kafa bisa tsarin shiyya.
“Za ta karbi kudade daga asusun tarayya, gudunmawa daga abokan haɗin gwiwar ci gaba, da sauransu, don magance nakasun kayan aiki da magance matsalolin muhalli a yankin,” in ji shi.
Majalisar dattijai bayan da Shehu ya gabatar da shi, ya zama kwamitin na gaba daya don yin magana ta hanyar yin la’akari da batun kudirin bayan an karanta shi a karo na uku.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Santa Barau Jibrin (APC-Kano), wanda ya jagoranci zaman majalisar bayan amincewa da kudirin ya yabawa kwamitin da Sanata Kaka ya jagoranci gudanar da kudirin.
Barau ya ce hukumar raya Kudu maso Yamma kamar sauran da aka kafa kwanan nan, za ta magance kalubalen samar da ababen more rayuwa da muhalli a yankin Kudu maso Yamma.
“Asalin kwamitocin raya kasa daban-daban da ake kafawa, shi ne a hanzarta bin diddigin ci gaban kasar baki daya.
“Shugaba Bola Tinubu ya amince da irin wannan kudiri da aka gabatar don cigaban shiyyar kuma tabbas zai amince da wannan,” in ji shi.(NAN) (www.nannews.ng)
KC/AMM
========
Abiemwense Moru ne ya gyara