Kwarewar aiki: Ma’aikatan Lafiyar Jihar Bauchi sun ziyarci takwarorinsu a jihar Filato
Kwarewar aiki: Ma’aikatan Lafiyar Jihar Bauchi sun ziyarci takwarorinsu a jihar Filato
Lafiya
By Blessing Odega
Jos, Janairu 14, 2025 (NAN) Tawagar Hukumar Kiwon Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi, sun halarci Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Filato, domin inganta ayyukanta, da samar da hadin gwiwa tsakanin jihohi da raba ilmi.
Kwamishinan lafiya na jihar Filato, Dr Cletus Shurkuk, a lokacin da yake karbar tawagar da suka kai masa ziyarar ban girma a Jos, ya ce binciken wani muhimmin mataki ne na samar da ingantaccen ilimi da sanin makamar aiki a tsakanin jihohin biyu.
Shurkuk ya ce binciken zai kuma kari ga inganta harkokin kiwon lafiya a jihohin biyu, musamman a matakin farko.
Tun da farko, Dokta Adamu Mohammed, daraktan kula da rigakafin cututtuka na hukumar lafiya matakin farko na jihar Bauchi, wanda ya jagoranci tawagar ya ce sun kai ziyarar ne da nufin nazarin ayyuka da tsarin hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Filato.
Mohammed ya ce wakilan sun gudanar da zaman tattaunawa tare da ziyarce-ziyarce a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar.
A cewarsa, fahimtar juna da ra’ayoyin da aka yi amfani da su za su taimaka wajen inganta ingantaccen aikin kiwon lafiya a matakin farko. (NAN) ( www.nannews.ng)
UBO/WAS
Edited by ‘Wale Sadeeq