Kwalara: Mutum 4 sun mutu, 36 a asibitocia a jihar Adamawa
Kwalara: Mutum 4 sun mutu, 36 a asibitocia a jihar Adamawa
Kwalara
Daga Ibrahim Kado
Yola, Satumba 15, 2024 (NAN) Gwamnatin karamar hukumar Yola-Arewa ta jihar Adamawa ta sanar da bullar cutar kwalara a yankin.
Har ila yau, ta ce barkewar cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutane hudu yayin da wasu mutane 36 da suka kamu da cutar ke samun kulawa a asibitoci daban-daban a yankin.
Mista Jibrin Ibrahim, Shugaban Majalisar ne ya sanar da hakan ga manema labarai yayin ziyarar da ya kai wa wadanda suka kamu da cutar a Cibiyar Kula Cututtuka (IDC), Yola ranar Lahadi.
Ya ce an samu bullar cutar a sassan Alkalawa, Ajiya da Limawa da ke yankin.
“Akalla mutane 20 ne aka samu rahoton wadanda abin ya shafa da safe amma yanzu akwai sama da 40 da suka kamu da cutar kuma hudu sun mutu.
“Yawancin adadinsu an kwantar da su yayin da ma’aikatan kiwon lafiya ke kula da su”, in ji shi.
Ibrahim ya yaba da daukin gaggawa da ma’aikatan lafiya, Red Cross da abokan hulda na duniya suka yi.
A cewar sa, cutar da ake zargin ta barke ne sakamakon gurbataccen ruwa da ya taso daga ambaliya a wasu yankunan.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su kiyaye tsaftar muhallinsu, su tabbatar da shan ruwa mai tsafta da wanke kayan lambu da kuma ‘ya’yan itatuwa kafin a ci. (NAN) (www.nannews.ng)
IMK/KA
======
Kayode Olaitan ne ya gyara