Kungiyar CAN ta Arewa ta jajanta wa Sheikh Dahiru Bauchi, ya ce Najeriya ta yi rashin tarbiya

Kungiyar CAN ta Arewa ta jajanta wa Sheikh Dahiru Bauchi, ya ce Najeriya ta yi rashin tarbiya

Spread the love

Kungiyar CAN ta Arewa ta jajanta wa Sheikh Dahiru Bauchi, ya ce Najeriya ta yi rashin tarbiya

Daga Sani Idris Abdulrahman

Kaduna, Nov. 28, 2015 (NAN) Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya, sun nuna matukar alhininsu dangane da rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Bauchi, inda suka bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban rashi na ruhi da tarbiyya ga al’umma.

Sheikh Dahiru Bauchi, kamar yadda majiyar iyalansa ta bayyana, ya rasu ne a ranar Alhamis, yana da shekaru 98 a duniya.

A wani sakon ta’aziyya da ya fitar a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban kungiyar CAN ta Arewa, Rabaran Joseph Hayab, ya ce marigayi malamin na daya daga cikin malamai kalilan a kasar nan wadanda koyarwarsu ta ci gaba da karfafa zaman lafiya, tawali’u da mutunta juna ta fuskar addini.

Hayab ya kara da cewa, tsawon rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi da ya yi, musamman jajircewarsa wajen koyar da karatun kur’ani da tarbiya, ya samar da tsararrun dalibai da kuma bayar da gudunmawa sosai wajen inganta zamantakewar al’umma a Arewa.

Ya bayyana cewa kungiyar CAN ta Arewa ta amince da marigayi malamin a matsayin mutumin da ya yi amfani da karfinsa wajen karfafa zaman tare da hana tashe-tashen hankula ko da a lokutan tashin hankali a yankin.

A cewar shugaban kungiyar ta CAN, ta yi nuni da cewa rasuwar Sheikh Bauchi ta tunatar da ‘yan Najeriya game da bukatar da ke akwai na ganin an kiyaye dabi’un da ya ke wakilta, musamman a daidai lokacin da al’ummar kasar ke fama da rarrabuwar kawuna, rikicin siyasa da karuwar rashin tsaro.

Hayab ya kara da cewa kungiyar CAN ta Arewa za ta ci gaba da bayar da goyon baya na gaskiya da nufin samar da hadin kai da kuma tabbatar da cewa al’ummomin addinai biyu za su ba da gudunmawa mai ma’ana ga zaman lafiya da ci gaban Nijeriya.

Ya kuma jaddada cewa, karramawar da ta fi dacewa ga marigayi malamin ita ce ‘yan Nijeriya su kara jaddada aniyarsu ta samar da zaman lafiya, hakuri da hadin kan kasa.

Hayab ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, kungiyar Tijjaniyya, Masarautar Bauchi da sauran al’ummar Musulmi a fadin kasar nan.

Ya bukaci al’ummar Musulmi da Kirista da su kalli wannan lokaci a matsayin wata dama ta zurfafa tattaunawa tsakanin addinai da kuma sake gina aminci a tsakanin kungiyoyi daban-daban.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan duk wanda ke cikin bakin ciki, ya kuma baiwa marigayi malamin hutu na dindindin.(NAN)(www.nannews.ng)

SA/BRM

==========

Edited by Bashir Rabe Mani


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *