Kotu ta yanke wa wani mai gadi hukunci kan yin lalata da ‘yar shekara 14
Kotu ta yanke wa wani mai gadi hukunci kan yin lalata da ‘yar shekara 14
Hukunci
Daga Ramatu Garba
Kano, Feb. 17, 2025 (NAN) A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yanke wa wani mai gadi, Abubakar Muhammad, mai shekaru 50 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin yin lalata da diyarsa mai shekaru 14 da haihuwa.
Muhammad, wanda ke zaune a unguwar Wailari Quarters da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, an
yanke masa hukunci ne bayan ya amsa laifinsa.
Mai shari’a Mr S.M. Shu’aibu, ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi masa ba tare da wata shakka ba, don haka ta yanke hukuncin daurin shekaru bakwai ba tare da zabin tara ba.
Tun da farko, Mista Abdullahi Babale, mai shigar da kara na hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP), Kwamandan shiyyar Kano, ya shaida wa kotun cewa Muhammad ya aikata laifin ne a Wailari Quarters dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano a ranar 24 ga watan Janairun 2025.
Ya ce Muhammad ya yaudari diyarsa mai shekara 14 zuwa dakin matarsa da ke Wailari Quarters lokacin da matar
tayi tafiya zuwa Jigawa sai yayi lalata da ita.
Ya kara da cewa Muhammad yayi lalata da yarinyar har sau hudu a lokuta daban-daban, sai ya ba ta Naira 2,000 don
ta kara wa sana’ar wainar wake da takeyi.
Daga nan sai Babale ya gabatar da abubuwa guda biyu, da kuma shaidar yarinyar ga kotu domin tabbatar da kararsa.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 16(1) na dokar hana fataucin mutane (Haramta) tilastawa da gudanar da mulki na shekarar 2015, wanda aka hukunta a karkashin sashe na 26(1) na TIP ACT 2015.
Lauyan mai kariya, Mista I. I. Umar, ya roki a yi masa sassauci a madadin wanda ake tuhuma.(NAN)(www.nanmews.ng)
RG/HA
======
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta gyara