Karamar Hukumar Hadejia ta haramta da daukar fasinjoji barkatai
Karamar Hukumar Hadejia ta haramta da daukar fasinjoji barkatai
Parks
Daga Muhammad Nasir Bashir
Dutse, Jan. 13, 2025 (NAN) Majalisar karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa ta ce ta haramta duk wani wurin dauka da sauke fasinjoji maras izini a yankin domin rage cunkoso da sauran matsalolin tsaro.
Jami’in yada labarai na karamar hukumar, Alhaji Muhammad Talaki, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin.
Talaki ya ce an sanar da haramcin ne a cikin wata sanarwar da a fitar fitar a karshen taron kwamitin rage cunkoson ababen hawa na majalisar Hadejia a ranar Laraba a Hadejia.
“Kwamitin rage cunkoson ababen hawa na karamar hukumar Hadejia ya hana daukar fasinjoji da sauke kaya da lodin fasinjoji a wajen wuraren da aka amince da su a fadin yankin.
“Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Shugaban kwamitin kuma mai kula da Motoci na shiyyar, Alhaji Sani Barde, ya fitar jim kadan bayan kammala taron kwamitin da ma’aikata da ma’a sana’ar sufuri da kuma kungiyoyin ‘yan kasuwa na yankin.
“Saboda haka, ana umurtar motocin haya da kananan motocin bas da su dauko da sauke fasinjojin su kawai a wuraren da gwamnati ta amince da kuma ta kebance tasha a yankin karamar hukumar,” in ji shi.
Talaki ya bayyana cewa an yanke shawarar ne bayan dogon nazari kan yadda za a rage cunkoson ababen hawa da ke haddasa yawaitar hadurra a tituna da kuma rashin bin ka’ida a yankin.
Ya ce, kwamitin ya kuma amince cewa, daga yanzu duk wani direban mota da aka kama yana tukin mota da hadari a kowace hanya a yankin, musamman a lokacin daurin aure, za a gurfanar da shi a gaban kuliya.
A cewarsa, duk wani ko direban da aka samu yana lodin fasinja ko lodi kaya gefen hanya da kuma daukar fasinja saman ababan hawa za a gurfanar da shi gaban kotu.
“Kwamitin ya kuma yanke shawarar cewa direbobin da ke da hannu wajen shan miyagun kwayoyi, gudu wuce kima da kuma wadanda ba su kai shekaru ba za su fuskanci fushin doka.
“Har ila yau, kwamitin ya amince da soke duk izinin rumfunan wucin gadi a kan manyan tituna a yankin kuma ya shawarci wadanda ke da irin wannan izini su tuntubi majalisar don sabunta,” in ji shi.
Talaki ya yi nuni da cewa, “an dauki kwakkwaran matakai ne domin rage yawan hadurran tituna tare da dakile cunkoson ababen hawa domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
Sanarwar ta bayyana cewa taron ya samu halartar wakilan hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya na yankin. (NAN) (www.nannews.ng)
MNB/GOM/USO
Gregg Mmaduakolam/Sam Oditah ya gyara