Kamfanin siminti na BUA ya horar da matasa 60 akan sarrafa motoci na musamman
Kamfanin siminti na BUA ya horar da matasa 60 akan sarrafa motoci na musamman
Horowa
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Aug. 5, 2025 (NAN) Kamfanin siminti na BUA, Kalambaina – Sokoto, a ranar Litinin ya kaddamar da shirinsa na ‘Host Communities Empowerment Scheme’, tare da horas da matasa sittin akan tukin motoci na musamman daga al’ummomin da suke karbar bakuncinsa.
Manajan Darakta na kamfanin, Mista Yusuf Binji, ya ce an yi shirin ne domin ba su kayan aiki don samun sana’o’in yi a kamfanin da ma sauran wurare.
Binji, wanda ya samu wakilcin Daraktan Ayyuka, Mista Aminu Bashar, ya ce a lokuta daban-daban, kamfanin ya yi tallar ayyukan yi, inda ya kara da cewa, “duk da haka, mafi yawan mutanen da suka fito daga yankunan da aka kafa kamfanin ba su iya neman aikin ba.
Ya ce an tsara shirin ne domin karfafawa matasan yankin ta hanyar basu sana’o’in dogaro da kai wajen gudanar da ayyuka na mussamman, da suka hada da tuki, gyare-gyare, da kula da na’urori.
Ya ce za a kuma baiwa wadanda aka horas din damar gudanar da na’urorin tona a wuraren da ake katange da sauran su.
A cewar Binji, an gudanar da atisayen na tsawon watanni shida kuma kowane mai cin gajiyar shirin zai rika karbar Naira 150,000 duk wata a matsayin alawus na horo.
Ya bayyana shirin a matsayin wata dama ce da ba kasafai ba ga mahalarta taron don samun kwarewa mai mahimmanci da kuma samar da aiki mai ma’ana a kasuwar hada-hadar aiki ta zamani.
Ya ce a karshen atisayen za a ba wa wadanda aka horas din damar zabar aiki da kamfanin ko kuma neman aikin yi a wasu wurare.
Manajan daraktan ya bayyana fatansa cewa za a ci gaba da gudanar da atisayen tare da fadada shi zuwa wasu hidimomi domin al’ummomin da ke karbar bakuncin su ci gajiyar kasancewar kamfanin a yankinsu.
A nasa jawabin Manajan Quarry, Muhammad Chinoko, ya ce wannan atisayen ya dace da matasa, inda ya ce hakan zai kara kaimi da kuma jawo hankalin wasu da za su yi takara a wannan kamfani.
Da yake jawabi a madadin wadanda suka samu horon, Attahiru Ladan, daga unguwar Asare, ya godewa kamfanin bisa wannan dama da aka ba su, ya kuma ba da tabbacin za su yi iya kokarinsu wajen koyo da gudanar da sana’o’in.
Ladan ya ce ko shakka babu wannan damar za ta inganta jin dadin su da ma ‘yan uwansu.
Ya bayyana horon a matsayin wani shiri na kawo sauyi a rayuwa, inda ya yaba da irin tasirin da kokarin da kamfanoni ke yi na kula da jama’a a kan al’ummomin da ke karbar bakuncinsa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya shaida yadda aka gabatar da shawarwarin kare lafiya, tattaunawa kan bunkasa albarkatun dan adam da sauran batutuwa. (NAN) ( www.nannews.ng )
HMH/BRM
=========
Edited by Bashir Rabe Mani