Jihar Kaduna ta fadada hanyoyin karkara domin bunkasa noma

Jihar Kaduna ta fadada hanyoyin karkara domin bunkasa noma

Spread the love

 

Hanya

 

By Mustapha Yauri

 

Zaria (Jihar Kaduna) Satumba 8, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Kaduna ta fara aikin gina titunan karkara a fadin jihar domin bunkasa harkokin noma a jihar.

Yunkurin dai na nufin saukaka zirga-zirgar kayan amfanin gona, tare da inganta kasuwannin manoma da kuma karfafuwar samar da abinci a fadin jihar.

Babban sakataren ma’aikatar noma, Alhaji Umar Abba ne, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Zariya, cewa, shirin na da nufin rage asarar da ake samu bayan girbi.

Ya ce, gwamnatin Gwamna Uba Sani, ta jajirce wajen samar da hanyoyin shiga karkara, domin karfafa ayyukan noma da bunkasa zamantakewa da tattalin arziki, tare da ci gaban al’umma baki daya.

Abba ya kara da cewa, shirin na hadin gwiwa ne tsakanin bankin duniya da gwamnatin jihar Kaduna, a karkashin shirin samar da ayyukan noma na karkara (RAAMP).

Babban sakataren ya ci gaba da cewa, a kwanakin baya ma’aikatar ta gudanar da ziyarar gani da ido, a kashi na biyu na wasu al’ummomin da suka ci gajiyar ayyukan hanyoyin.

Sakataren ya bukaci ‘yan kwangila, da su kammala ayyukan cikin gaggawa tare da kiyaye ka’idoji.

Hakazalika, Ko’odinetan ayyukan, Malam Zubairu Abubakar, ya zayyana wasu daga cikin ayyukan hanyoyin da ake gudanarwa a matakai daban-daban.

Ya ce sun hada da tituna Sama da kilomita 50 na Fala zuwa Sayasaya, Masama Gadas zuwa Anchau Road a karamar hukumar Ikara.

Sauran in ji shi, sun hada da titin Gora zuwa Kwoi, mai tsawon kilomita 3.5 a karamar hukumar Jaba, sannan titin Aduwan Gida zuwa Fadan Kaje mai nisan kilomita 5.6 a Zonkwa.

Akwai kuma na karamar hukumar Zangon Kataf da titin Illa zuwa Kofato, mai kilomita 13.4 a karamar hukumar Igabi da titin Sabon Tasha zuwa Juji zuwa Unguwar Barde da sauransu.

A cewar mai gudanar da aikin, duk ayyukan hanyoyin shiga karkara karkashin RAAMP, za a kammala sune a karshen shekarar 2025.

Don haka, ya yi kira ga mazauna yankin da masu amfani da hanyoyin, da su ci gaba da bada hadin kai ga ‘yan kwangilar, domin kammala da ayyukan cikin sauki da kuma dace. (NAN) (www.nannews.ng)

 

AM/KLM

Fassarar Aisha Ahmed

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *