Jami’ar ABU ta baiwa dalibai 107 tallafin karatu

Jami’ar ABU ta baiwa dalibai 107 tallafin karatu

Spread the love

 

Jami’ar ABU ta baiwa dalibai 107 tallafin karatu

By Mustapha Yauri

Scholarship

Zaria (Jihar Kaduna) Satumba 2024 (NAN) Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, ta bayar da tallafin karatu ga dalibai ‘yan kasaahen waje 107, marasa galihu da dalibai masu bukata ta musamman, kamar yadda wani jami’i ya bayyana.

Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na Jami’ar Auwalu Umar ya fitar a ranar Juma’a a Zariya, ta ce daliban kasashen waje 49 da suka kammala karatun digiri na biyu ne suka ci gajiyar shirin.

Umar ya kara da cewa, sauran sun hada da dalibai 42 da ke karatun digiri na farko a kasashen waje, daliban Najeriya 10 da kuma dalibai shida marasa galihu.

Ya ce Farfesa Kabiru Bala mataimakin shugaban jami’ar ABU a lokacin da yake gabatar da wasikun tallafin ga wadanda suka ci gajiyar shirin ya ce shirin ya yi daidai da muradin shugabannin jami’ar.

Ya kuma kara da cewa, mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana cewa an bude kofofin jami’ar ga maza da mata daban-daban, don haka ne jami’ar ta bada tallafin ga dalibai masu rauni.

Bala, wanda mataimakin shugaban sahen ilimi, Farfesa Raymond Bako ya wakilta, ya kara da cewa tallafin ba wai tsabar kudi a ke zubawa ba, ya kasance ta kowacce hanya don tallafa wa dalibai da su ka yi fice.

Ya ce: “A koyaushe akwai kwarewa a cikin nakasa, suna iya komai kamar sauran ɗaliban da ke da buƙatu na musamman.”

Mataimakin shugaban jami’ar ya umurci daliban kasashen waje da su kasance jakadu nagari na jami’ar a kasashensu bayan kammala karatunsu.

Sanarwar ta kuma ruwaito Daraktar cibiyar bayar da shawarwari da ci gaban bil’adama, Dakta Sa’adatu Muhammad-Makarfi, tana cewa jami’ar ta yanke shawarar da daliban kasashen waje wadanda suke da digiri na farko da na biyu su na biyan kudi daidai da na daliban ‘yan asalin kasar.

Wannan a cewarta, na da nufin rage musu nauyi saboda tabarbarewar tattalin arzikin Kasa. 

Muhammad-Makarfi ya ce ga daliban da ke da bukata ta musamman jami’ar ta biya wa wasu cikakkun kudaden karatu da masauki, yayin da wadanda suka biya kudin karatu jami’ar ta biya musu masauki.

Shima da yake nasa jawabin, shugaban dalibai masu bukatu na musamman Mustapha Yahaya ya nuna jin dadinsa ga jami’ar da suka duba halin da suke ciki.

Yahaya ya ce daliban da ke da bukatu na musamman a jami’ar sun haura sama da 15, yayin da ya yi kira ga mahukuntan jami’ar da su kara wa wasu tallafin karatu. (NAN) (www.nanews.ng)

AM/KLM

======

Muhammad Lawal ne ya 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *