Jami’an tsaro sun kama alburusai 610 a Katsina

Jami’an tsaro sun kama alburusai 610 a Katsina

Spread the love

Jami’an tsaro sun kama alburusai 610 a Katsina

Harsashi
Zubairu Idris
Katsina, Satumba 11, 2024 (NAN) Rundunar tsaron Al’umma mai taimakawa jihar Katsina, Community Watch Corps, ta cafke wata mota makare da alburusai 610 a karamar hukumar Batsari da ke jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dr Nasir Muazu, ya fitar a ranar Laraba a Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Batsari na daga cikin kananan hukumomin da ke kan gaba wajen fuskantar matsalar rashin tsaro a jihar.
“Jami’an mu sun gudanar da wani gagarumin aikin tsaro a ranar 10 ga Satumba, 2024, da misalin karfe 7:30 na dare a garin Batsari.
“A bisa ga sahihan bayanan sirri, ‘yan kungiyar da ke sa ido kan al’umma sun kama wata motar kasuwanci mai lamba BTR 45 XA, dauke da fasinjoji 17 – mata 13 da maza hudu, ciki har da direban motar.
“A lokacin da jami’an tsaron suka gudanar da binciken akai-akai a wani shingen binciken ababen hawa, sun gano tarin alburusai da aka boye a karkashin kujera, wanda daga baya aka gano tana dauke da harsasai 610 na AK-47 da kuma Janar Purpose Machine Gun (GPMG), da kuma mujallu biyu,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce wanda ake zargi da mummunan aikin yana sanye da fararen kaya ne, wanda ya nuni samun shakku ga masu ababen hawa a lokacin da tafiye tafiye. 
“Da farko ya mutumina ya dage da zama a bayan motar kuma ya bayyana a fili bai ji dadi ba kuma cikin damuwa lokacin da aka tsayar da motar don dubawa.
“Wanda ake zargin ya yi nasarar tserewa, inda ya bar alburusai da ke boye,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar karkashin Gwamna Dikko Radda ta dukufa wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da bayar da goyon baya da kuma kara karfin jami’an tsaronta domin yakar duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar. (NAN) ( www.nannews.ng )
ZI/KLM
=====
Muhammad Lawal ne ya gyara

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *