Hukumar NDLEA ta kama matashi dauke da tarin wiwin Akuskura a Kano

Hukumar NDLEA ta kama matashi dauke da tarin wiwin Akuskura a Kano

Spread the love

Hukumar NDLEA ta kama matashi dauke da tarin Akuskura a Kano

Akuskura
Daga Ramatu Garba
Kano, Satumba 2, 2025 (NAN) Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kano, ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 37, Ali Muhammad, dauke da kwalaben Akuskura 8,000 (garin ganye) da kuma sunki 48 na tabar wiwi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mista Sadiq Muhammad-Maigatari, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya
fitar ranar Talata a Kano.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 28 ga watan Agusta, a kusa da Gadar Tamburawa, kan hanyar Zariya zuwa Kano, a lokacin da aka tsaya ana bincike, a lokacin da yake jigilar kaya daga Legas kan hanyar zuwa Maiduguri.

A cewarsa, haramtattun abubuwan an boye su ne a cikin wata tirela cike da kekuna masu uku (Keke Napep).

“An boye miyagun abubuwan ne a tsakanin kekuna masu kafa uku da kuma karkashin tirelar, inda aka gina murfin katako don boye kayan.

“Jami’an NDLEA sun gano wannan boye ta hanyar himma da jajircewa,” in ji shi.

Muhammad-Maigatari ya ce an tsare wanda ake zargin ana kuma ci gaba da gudanar da bincike tare binciken dakin gwaje-gwaje don tabbatar da yanayin abubuwan.

Ya kara da cewa kwamandan hukumar ta NDLEA, reshen jihar Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya yaba da goyon bayan da
shugaban hukumar ta NDLEA, Retired Brig.-Gen. Buba Marwa, wajen karfafa ayyuka a fadin kasar nan.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk wani motsi ko kayan da ake zarginsu
da shi zuwa ofishin hukumar NDLEA mafi kusa ko kuma wasu hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa. (NAN)(www.nannews.ng)
RG/KLM

========
Muhammad Lawal ne ya gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *