Hukumar alhazai ta jihar Kano ta fara horarda maniyatan aikin hajjin 2025
Hukumar alhazai ta jihar Kano ta fara horarda maniyatan aikin hajjin 2025
Horo
Daga Bosede Olufunmi
Kano, Janairu 21, 2025 (NAN) Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta fara horas da maniyata aikin Hajji na 2025 a cibiyoyi tara cikin fadin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Dederi, ya sanyawa hannu kuma ya raba wa manema labarai a ranar Talata a Kano.
Dederi ya nakalto Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Danbappa, ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da Malamai wadanda za su jagoranci kwas din karawa juna ilimi a cibiyoyi daban-daban a fadin jihar.
Shugaban wanda Daraktan gudanarwa da ayyuka na kasa, Alhaji Yusif Muktar, ya wakilta ya ce cibiyoyin sun hada da; Bichi, Dogowa, Gwarzo, Makarantar
Nazarin Larabci, Rimin Gado, Gezawa, Kura, Rano da Wudil.
Danbappa ya nemi addu’o’i daga Malamai a fadin jihar domin samun nasarar gudanar da aikin Hajjin 2025.
Ya shawarci dukkan maniyyatan da suke son zuwa aikin Hajji da su yi kokarin halartar kwas din karawa juna ilimi a cibiyoyinsu domin samun karin ilimi a kan ka’idojin aikin Hajji. (NAN)(www.nannews.ng)
BO/KLM
=======
Muhammad Lawal ne ya gyara