Hajj 2025: Jigawa ta tanadi masaukin maniyyata
Hajj 2025: Jigawa ta tanadi masaukin maniyyata
Masauki
Daga Muhammad Nasir Bashir
Dutse, Jan. 20, 2025 (NAN) Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta samu masaukin maniyyata aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.
Kakakin hukumar, Malam Habibu Yusuf, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Litinin a Dutse, ya bayyana cewa ginin ba shi da nisan tafiya daga Muharram (Masallacin Harami) da ke Makkah.
Yusuf yace “hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta samu nasarar samar da ingantaccen otal domin maniyyata aikin hajjin 2025.
“Otal din da ke Darakun, yana da tazarar mita 800 zuwa Masallacin Harami na Makkah.
“Wannan nasarar ta nuna kudirin hukumar na tabbatar da aikin Hajji mai inganci ga alhazan jihar Jigawa.”
Ya kara da cewa babban daraktan hukumar, Alhaji Ahmad Labbo, ya bukaci masu sha’awar halartar aikin hajjin 2025 da su tabbatar da biyansu
kudaden ajiya a kan lokaci.
A cewarsa, Labbo ya jaddada mahimmancin biyan kudi da wuri domin hakan zai kawo saukin tsare-tsare da dabaru na aikin hajji.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ta tuna cewa a kwanakin baya ne hukumar ta sanar da ranar 30 ga watan Janairu, wa’adin rajistar dukkan maniyyatan aikin hajjin shekarar 2025 a fadin kasar.
Hukumar ta bayyana cewa gyara da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta yi na kalandar shekarar 2025 ta umurci hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da su fitar da duk abin da aka tara kafin ranar 1 ga watan Fabrairu.
NAN ta kuma ruwaito cewa NAHCON ta ware kujeru 1,518 ga jihar don gudanar da aikin hajjin 2025, yayin da a baya hukumar ta umurci maniyyatan jihar da su biya Naira miliyan takwas da dubu ɗari huɗu har zuwa lokacin da hukumar ta NAHCON ta bayyana a hukumance na biyan kudin aikin hajjin 2025.(NAN)(www.nannews.ng)
MNB/ACA/HA
============
Chidinma Agu da Hadiza Mohammed-Aliyu ne suka gyara