Gwamnatin tarayya ta yi karar Sowore, Facebook, X, bisa zargin cin zarafin shugaba Tinubu a yanar gizo

Gwamnatin tarayya ta yi karar Sowore, Facebook, X, bisa zargin cin zarafin shugaba Tinubu a yanar gizo

Spread the love

Kara
Daga Taiye Agbaje

Abuja, Satumba 18, 2025 (NAN) Gwamnatin tarayya ta maka wani dan siyasa, Omoyele Sowore a kotu, bisa zarginsa akan zagin shugaban kasa Bola Tinubu, ta yanar gizo.

Gwamnatin, a cikin kundi din mai alamar FHC/ABJ/CR/484/2025, ta maka kamfanin Meta (Facebook) Incorp. da X Inc. a matsayin wadanda ake tuhuma a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Mohammed Abubakar, Daraktan shigar da kararraki na ma’aikatar shari’a ta tarayya ne, ya shigar da karar mai kwanan wata 16 ga watan Satumba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, a tuhume-tuhume biyar, Sowore, wanda mawallafin ne na jaridar Sahara Reporters, ana zarginsa da yin ikirarin karya a kan shugaban kasa ta hanyar kiransa da “mai laifi.”

An shigar da karar ne kwanaki kadan bayan da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta bukaci a janye sakon da aka wallafa a shafin Facebook da X (tsohon Twitter), wanda ake zargin Sowore ya yi amfani da su wajen bata sunan.

Sowore, wanda dan takarar shugaban kasa na ne a jami’iyyar African Action Congress (AAC) a shekarar 2019 da 2023, ana zarginsa da sabawa
tanade-tanaden dokar laifuka ta Intanet (Hana, Rigakafi, da sauransu) gyaran fuska, 2024.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen da ake zargin Sowore, a ranar 25 ga watan Agusta, ya yi amfani da shafinsa na X — @Yele Sowore, wajen aika sakon.

A cewar sakon “WANNAN MAI LAIFI @ Official PBAT GASKIYA YA JE BRAZIL YANA CEWA BABU CIN CIWANCI A
KARKASHIN MULKINSA A NIGERIA. WANNAN GIRMAN KARYA BA KUNYA!”

Sakon na karya, an saka shi ne “domin haifar da tabarbarewar doka da oda a tsakanin daidaikun mutane, masu ra’ayi daban-daban.

Haka kuma sakon an yi shi ne domin taba mutuncin shugaban kasa kuma kwamandan rundunar sojojin Tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (GCFR).”

Laifin dai an ce ya sabawa sashe na 24 (1) (b), na dokar hana aikata laifuka ta Intanet da aka yiwa gyara a shekarar 2024, da dai sauransu.(NAN)(www.nannews.ng)
TOA/SH

=======
Sadiya Hamza ce ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *