Gwamnatin Tarayya ta jajantawa Gwamna Bago, al’ummar Nijar bisa fashewar tankar mai
Ta’aziyya
By Collins Yakubu-Hammer
Abuja, Oktoba 23, 2025 (NAN) Gwamnatin tarayya ta jajanta wa gwamnati da al’ummar Neja bisa fashewar wata tankar man fetur a garin Essa, da ke karamar hukumar Katcha a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar ranar Alhamis a Abuja
Takardar ta bayyana matukar alhininsa bisa afkuwar lamarin da yayi sanadin salwantar rayuka da kuma jikkata wasu da dama.
“Muna tare da gwamnati da al’ummar jihar Neja wajen jimamin wannan rashi.
“Wannan lamari mai ratsa zuciya, ya sake haifar da mummunar illar hadurran tankar mai a cikin al’ummarmu.
“Gwamnatin tarayya, ta yi bakin cikin cewa, duk da cigaba da wayar da kan jama’a tare da gargadi game da illolin kwasar man fetur daga fadowar tankunan man fetur, har yanzu wasu na yin kasadar da ke barazana ga rayuwa.
“Kowane ran dan Najeriya yana da daraja, kuma irin wadannan bala’o’in za a iya kauce musu sun zama izina domin ƙarin kulawa da bin umarnin tsaro,” in ji Idris.
Ya yaba da yadda gwamnatin Neja, hukumomin tsaro da masu bada agajin gaggawa, suka gaggauta daukar matakin kashe gobarar, tare da ceto wadanda suka tsira da rayukansu, kuma suka bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Ministan ya ce an kuma umurci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), da ta kara kaimi akan kokarin da gwamnatin jihar ke yi na samar da agaji da magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu.
“Gwamnatin tarayyar ta kuma umurci hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, da ta kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a fadin kasar.
“A kara tsaurara matakan tsaro, musamman a yankunan karkara da masu fama hadariurra, domin hana sake afkuwar irin wannan bala’i.
“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da wadanda abin ya shafa tare da iyalansu, da daukacin al’ummar Neja a wannan lokaci na bakin ciki.
“Allah Ya jikan wadanda suka rasu, kuma Allah Ya bawa ‘yan’uwansu ikon jure wannan rashi mai raɗaɗi,” in ji Idris. (NAN) (www.nannews.ng)
CMY/BEKl/BRM
==============
Edited by Abdulfatai Beki/Bashir Rabe Mani
Fassarar Aisha Ahmed

