Gwamnatin Katsina ta amince da kashe naira miliyan ashirin don gyaran makabartu a kananan hukumomi, albashin Hakimai.
Gwamnatin Katsina ta amince da kashe naira miliyan ashirin don gyaran makabartu a kananan hukumomi, albashin Hakimai.
Makabarta
Zubairu Idris
Katsina, Aug. 29, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Katsina ta amince wa kowace karamar hukuma ta kashe kudi naira miliyan 20 domin gyara makabarta a yankinta.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya daga Masarautar Katsina da Daura ranar Alhamis a Katsina.
Ya bayyana shirin a matsayin hidima ga jama’a da kuma hanyar neman albarkar Allah ga jihar.
Radda ya kuma sanar da wani sabon tsarin jin dadin jama’a don karfafawa sarakunan gargajiya da malaman addini a jihar.
Ya bayyana cewa a sabuwar dokar da Majalisar Dokokin Jihar ta kafa, “yanzu dukkan Hakimai za su rika karbar albashin da bai gaza mataki na 16 ba.
“Bugu da kari, Hakimai 6,652 a fadin jihar za su rika karbar alawus-alawus na wata-wata yayin da sama da Limamai 3,000 da mataimakansu daga Masallatan Juma’a za a tallafa musu da alawus.
“Bugu da kari kuma ‘yan kungiyar Izala da na Darika a kowace karamar hukuma 34 za su ci gajiyar alawus-alawus”.
Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na tunkarar matsalar rashin tsaro gaba-da-gaba, yana mai nuni da cewa tsaro shi ne babban abin da gwamnatin sa ta sa a gaba.
A cewarsa, ya zuwa yanzu an horar da sama da matasa 1,500 domin tallafa wa kokarin tsaro domin dakile kalubalen rashin tsaro da ke addabar jihar.
Ya ce matasan, an yi musu cikakkun kayan sawa, da riguna, da kayan aiki.
Don haka, Gwamna Radda ya bukaci sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da su kara wayar da kan jama’a, yana mai tunatar da ‘yan kasar cewa su fara taimakon kansu kafin gwamnati ta sa baki a samu sakamako mai dorewa.
“Tsaro wani nauyi ne na hadin gwiwa, dole ne mu hada kai don kare mutanenmu,” in ji shi.
Tun da farko, Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar, wanda Hakimin Baure, Alhaji Daha Umar-Farouq ya wakilta, ya jaddada goyon bayansu a sakamakon hadarin mota da gwamnan ya yi a Daura.
Shima da yake nasa jawabin, Wazirin Katsina Sen. Ibrahim Ida, wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir-Usman, ya yabawa gwamnan bisa jajircewarsa na mayar da masarautun biyu matsayi mafi girma.
Ya kara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta bullo da su ya dawo da martabar cibiyoyin gargajiya tare da karfafa rawar da suke takawa wajen gudanar da mulki da ci gaban al’umma.
Majalisar Masarautar ta kuma kara da cewa, za ta ci gaba da baiwa gwamnati goyon baya ta hanyar addu’o’i da hadin kai domin samar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a fadin jihar nan.(NAN) www.nannews.ng
ZI/MNA
Maureen Atuonwu ta gyara