Gwamnatin jihar Jigawa ta hada gwiwa da kamfanin Saudi Arabiya don bunkasa noman dabino

Gwamnatin jihar Jigawa ta hada gwiwa da kamfanin Saudi Arabiya don bunkasa noman dabino

Spread the love

Gwamnatin jihar Jigawa ta hada gwiwa da kamfanin Saudi Arabiya don bunkasa noman dabino

Dabino
Daga Aisha Ahmed
Dutse, Feb. 11, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Jigawa ta hada gwiwa da kungiyar samar da dabino ta Saudi Arabiya da kamfanin Netay Agro-Tech mai sana’ar noma da ke Najeriya domin bunkasa noman dabino a jihar.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin
noma na kasar Saudiyya wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki.

Jagoran tawagar, Mista Abdul’aziz Abdurrahman-Al-Awf, ya nanata kudirin kungiyar na kawo sabbin dabarun noma na zamani a Jigawa.

Ya ce “muna son tabbatar da samar da dabino a duk shekara, maimakon noman dabino na kan lokaci kuma hadin gwiwarmu za ta kunshi
horar da manoma da yawa, da karfafa matasa.

“Muna kuma son gabatar da wasu nau’in dabino mafi daraja da yawan amfanin gona a kasar Saudiyya da za a noma a Jigawa.”

Babban makasudin ziyarar, in ji shi, ita ce tattaunawa kan dabarun hadin gwiwa don bunkasa noman dabino a Jigawa ta hanyar bunkasar fasahar noma, fasahar zamani da zuba jari a fannin noma.

Ya kara da cewa “wannan hadin gwiwa ba wai kawai zai kara yawan dabino da ake nomawa a Jigawa ba, har ma zai inganta inganci, wanda hakan zai sa jihar ta zama cibiyar noman dabino a Najeriya da Afrika.”

Da yake mayar da martani, Namadi ya bayyana goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa ya dace da tsarin bunkasa noma na jihar.

Ya ce “muna maraba da ku zuwa jihar Jigawa kuma mun yaba da sha’awar ku na yin aiki da mu. A matsayinmu na gwamnati mun jajirce sosai
wajen wannan hadin gwiwa domin zai amfani al’ummarmu matuka.

“Ziyarar ku da kuma shirye-shiryen ku na hadin gwiwa da mu wajen samar da noman dabino a fadin jihar, tare da inganta noman alkama, sun yi dai dai da
burinmu na bunkasa noma.”

Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin sa na samar da kayan aiki da suka dace domin tabbatar da gudanar da aikin cikin nasara tare da bayyana
kwarin gwiwar cewa hadin gwiwar za ta haifar da gagarumin alfanu da kuma matsayin jihar Jigawa a matsayin wadda ke kan gaba a harkar dabino
a duniya.

Abubakar Musa-Bamai na kamfanin Netay Agro-Tech, ya bayyana dimbin ayyukan da aka riga aka yi, wadanda suka hada da nazarin kasa da tuntubar juna da cibiyoyin bincike.

Ya sanar da cewa, nau’in dabino guda hudu da ake nema ruwa a jallo na Mejdool (Meju), Barhi (Bari), Sukkari (Sukari) da Ajwa, an bayyana su a matsayin wadanda suka dace domin noma mai yawa a Jigawa.

A yayin ziyarar, tawagar Saudiyya tare da wakilan kamfanin Netay Agro-Tech sun zagaya wurare daban-daban a fadin jihar.(NAN)(www.nannews.ng)
AAA/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *