Likitan dabbobi
Aisha Ahmed
07030065142
Miga (Jihar Jigawa), Satumba 27, 2024 (NAN) Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da cibiyoyin kula da lafiyar dabbobin na tafi da gidan ka a kananan hukumomi 27 na jihar.
A yayin bikin kaddamar da asibitocin tafi da gidanka a yankin Garbau da ke karamar hukumar Miga a ranar Juma’a, Namadi ya ce an tsara wuraren ne domin samar da ayyukan kiwon lafiyar dabbobi kyauta.
“Ta hanyar fadada hanyoyin kula da lafiyar dabbobi, ba wai muna kare lafiyar dabbobi ne kawai ba, har ma da inganta ayyukan noman mu.
“Kyakkyawan shanu na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin jiharmu kuma wannan shiri zai taimaka mana wajen bunkasa noman dabbobi.
Namadi ya ce: “Wannan shiri zai yi tasiri wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin noma a jihar, musamman ga al’ummar Fulani wadanda rayuwarsu ta dogara da lafiyar dabbobi.”
Ya bayyana muhimman abubuwan da shirin ya kunsa, wadanda suka hada da samar da babura, ayyukan kiwon lafiyar dabbobi kyauta, da kuma ci gaba da samar da magungunan dabbobi, domin inganta lafiyar dabbobi a fadin jihar.
“Kowace karamar hukuma za ta karbi babura guda biyar masu cikakken kayan aiki don tallafawa ayyukan kula da dabbobi,” in ji gwamnan.
An raba jimillar babura 235, baya ga makamantansu da ake da su, wadanda adadinsu ya kai 535 cibiyoyin kula da lafiyar dabbobi a fadin jihar.
Bugu da kari, Namadi ya jaddada cewa ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi a kowace karamar hukuma, za su yi tafiya zuwa yankunan makiyaya tare da ba da kulawa kyauta.
Ya kara da cewa, an yi hakan ne domin tabbatar da cewa Fulani makiyaya suna kula da shanu masu kyau, masu muhimmanci ga tsarin rayuwarsu da kuma tattalin arzikin jihar.
Har ila yau, gwamnan ya dorawa kansilolin kananan hukumomin da su tabbatar da samar da magunguna da alluran rigakafi, domin samun nasarar shirin na tsawon lokaci.
A nasa jawabin kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Mista Muttaka Namadi ya jaddada nasarorin da gwamnati mai ci ta samu wajen bunkasa noma.
Ya bayyana aikin dakunan shan magani na tafi da gidanka, a matsayin muhimmin kayan aiki da zai samar da tallafi ga makiyaya da sauran al’ummar jihar.
Wasu makiyayan da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, sun nuna jin dadinsu da wannan shiri, inda suka ce zai cece su da asarar dabbobi da dama.
Mista Musa Ardo, daya daga cikin su, ya ce makiyaya a jihar suna son samun cikkaken ribar dimokuradiyyar gwamnatin Namadi ta wannan karimcin.
Ya bayyana cewa ‘ya’yansu sun amfana da bayar da ilimin makiyaya da kuma ayyukan kiwon lafiya da rigakafi kyauta, “amma wannan shi ne karon farko da dabbobinmu suka fi maida hankali a kai.”
Har ila yau, Malam Haruna Tukur ya yabawa wannan karimcin tare da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ci gaba da gudanar da aikin. (NAN)
AAA/AOS
=======
Bayo Sekoni ne ya gyara shi