Gbajabiamila ya bukaci a inganta kular mahajjata
Hajji
Daga Salisu Sani-Idris
Abuja, Augusta 28, 2024 (NAN) Hon. Femi Gbajabiamila, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya jaddada bukatar yin garambawul a cikin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) domin dakile almundahana da kudade, sakaci da kuma musgunawa maniyyata.
Gbajabiamila ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai hedikwatar kula da aikin Hanji ta kasa wato NAHCON da ke Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ziyarar na daga cikin kokarin tattaunawa da hukumomin gwamnati a karkashin kulawar fadar gwamnati.
Ya ce bai kamata hukumar NAHCON ta shiga cikin wata rigima ba saboda muhimmacin aikinta da abin da take wakilta.
“Hukumar addini ce. Kwamiti ne da aka kafa don cika wajibai na addini da na ruhi ga maza da mata masu imani.
“Alhazai na tafiya kowace shekara domin sauke wani farilla na Musulunci. Ba wannan kadai ba, idan suna can, suna nan a matsayin jakadun Najeriya.
“A matsayinsu na jakadun Najeriya, ana sa ran za su dabbaka kishin kasarsu Najeriya, domin su wakilce mutanensu tare da nuna hali da dabi’a nagari.
“Mun yi nadamar yadda galibi ana cin zarafin alhazai saboda rashin tsari da NAHCON ke yi a lokacin aikin hajji,” in ji shi.
A cewarsa, a wasu lokutan alhazai ba sa gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba, don haka dole ne hukumar ta dauki nauyin gudanar da aikin hajjin cikin inganci a Najeriya da Saudiyya.
Ya kuma bukaci mahukunta da ma’aikatan hukumar da su hada kai da ofishin mataimakin shugaban kasa mai kula da hukumar domin gano kura-kuran da aka yi a baya, da yin gyara da kuma tabbatar da gudanar da ayyukan alhazai ba tare da wata matsala ba.
“Abin da ya faru ya faru, kuma muna nan don tsara hanyar da za a bi.
“Lokaci ya yi da za a sake fasalin tsarin hukumar ta yadda zai dace da ajandar sabunta salon muradai na Shugaba Bola Tinubu,” in ji shi.
Har ila yau, Sen. Ibrahim Hadejia, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya yi na’am da matsayin shugaban ma’aikatan, inda ya jaddada bukatar yin shiri da wuri domin aikin Hajji.
“Hajji babban aiki ne da ke bukatar tsari da kayan aiki. Na shiga cikin aikin 2024, kuma ɗayan mahimman darussan da aka koya shine buƙatar shiri da wuri.
“Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan alhazai daga Afirka, kuma muna da kasashen da adadinsu bai kai adadin mahajjata daga wata jiha a Najeriya ba.
“Hukumar Hajji tana kuma bukatar ta kara fito da gaskiya wajen sanar da mahajjata abin da suke biya,” in ji Hadeija.
Da yake mayar da martani, Prince Aliu Abdulrazak, Kwamishinan Zartarwa na Hukumar Kula da Ma’aikata da Kudi ta NAHCON, ya yi kira da a yi garambawul ga tsarin lissafin hukumar.
Ya kuma yi kira da a inganta wakilcin tarayya a cikin kungiyar.
“An kwatanta hukumar a matsayin ta kasa baki daya, amma tsarin wakilcin tarayya bai cika kammaluwa ba.
Abdulrazak ya ce “Idan ka shiga cikin jerin sunayen, wani yanki ne ya mamaye shi.”
Hakazalika, shugaban ma’aikatan ya ziyarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) inda ya jaddada bukatar sauya yadda ake tafiyar da aikin Jin Kai daga ib’til’i daga halin da ake ciki zuwa matakin da ya dace.
Ya kuma jaddada mahimmancin Shirin ko ta kwana kan rage kai Bata taimako bayan ib’til’i ya bayyana cewa za a iya kaucewa aukuwar bala’o’i da dama a kasar tare da kyakkyawan shiri da gargadin wuri.
“Hukumar NEMA tana da abubuwa biyu ne: rigakafin ib’til’i da rage bala’ai.
“Amma da alama mun fi mai da hankali kan ragewa tare da barin wani bangare na umarnin, wanda shi ne rigakafin.
“Dole ne mu kara duba fannin rigakafin saboda yawancin wadannan bala’o’i ana iya hana su,” in ji shi. (NAN) (www.nannews.ng)
SSI/SA
================femi gbajabiamila
Salif Atojoko ne ya gyara