Garin Maiduguri ya cika da ruwa yayin da madatsar ruwan Alau ta datse
Garin Maiduguri ya cika da ruwa yayin da madatsar ruwan Alau ta datse
Ambaliyar ruwa
By Yakubu Uba
Maiduguri, Satumba 10, 2024 (NAN) Mazauna Maiduguri a Borno sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama biyo bayan rushewar madatsar ruwa ta Alau da ta cika mako guda da ya gabata.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ya fitar a safiyar ranar Talata mai taken “Flooding Alert for Residents Bank of River” ta bukaci a kwashe mutanen da abun zai shafa cikin gaggawa.
Ya ce, “Saboda yawan ruwan da ba a saba gani ba a bana, muna kira ga daukacin mazauna bakin kogi da su dauki matakin kare kansu da dukiyoyinsu cikin gaggawa.
“Ruwan Alau Dam ya fasa wata tashar da a yanzu haka ke lalata gonaki kuma ruwan ya nufi gabar kogi.”
Tar ya kuma bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su bi hanyoyin ficewa domin tabbatar da tseratar da lafiyarsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a karo na karshe da madatsar ruwan ta samu irin wannan matsala shi ne a shekarar 1994, wanda hakan ya haifar da ambaliya da ba a taba ganin irinta ba a Maiduguri inda kusan rabin garin ya cika. (NAN) (www.nannews.ng)
YMU/BRM
==========
Edited by Bashir Rabe Mani