Cunkoso: Masu ruwa da tsaki sun bukaci alkalai su yi la’akari da zabin hukunci
Cunkoso: Masu ruwa da tsaki sun bukaci alkalai su yi la’akari da zabin hukunci
Cunkoso
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Agusta 29, 2024 (NAN) Kungiyar masu ruwa da tsaki kan gyara harkokin shari’a a jihar Sokoto sun bukaci alkalai da su yi la’akari da wasu zabuka na hukunta wadanda aka yankewa hukunci ba dauri ba a kowane lokaci.
Kiran na daga cikin kudurorin da Mr Rabi’u Gandi, wakilin kungiyoyin farar hula ya karanta a karshen taron masu ruwa da tsaki a ranar Laraba a Sokoto.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron mai taken “Fahimtar Dabarun Tsaretsaren Tsaro na Kasa, Samar da Ingantaccen Yanayi ga Ma’aikatan gwamnati da wadanda ba na Gwamnati ba”, wata kungiya ce mai zaman kanta ta CLEEN Foundation ce ta shirya tare da tallafi daga gidauniyar MacArthur.
Ya ce bisa la’akari da shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka bayar, akwai bukatar alkalai a kowane mataki su rika amfani da zabukan yanke hukunci kamar ayyukan al’umma da sauran hukunce-hukunce, ba zaman gidan yari ba a kodayaushe.
Ya bayyana cewa mafi yawan kashi na hukunce-hukuncen dauri sun sanya wuraren gyaran Hali cikin cunkoso, yana mai jaddada cewa yin amfani da zabin zai rage cunkoso.
Gandi ya kuma shawarci bangaren shari’a da ‘yan majalisar dokokin kasar da su saukaka tsarin sahhalewa masu laifi da sharadin kimtsuwa a mulkin kasar domin inganta tsarin.
Ya kuma kara jaddada mahimmancin tsarin sahhalewa fursunonin a Najeriya, wanda zai rage matsin lamba ga wuraren da ake tsare da su, da yawan barkewar gidan yari da korafe-korafe a tsakanin fursunonin.
A cewarsa, wakilan hukumomin tabbatar da doka a wurin taron sun ba da bayanai da shawarwari daban-daban kan mafi kyawun hanyoyin inganta ayyukansu da kuma kalubalen da suke fuskanta a kasar.
Yayin da ya yabawa gidauniyar CLEEN bisa wannan kokarin, Gandi ya ce za a tattara bayanan tare da mikawa hukumomi na gaba domin tantancewa da aiwatar da su.
Da yake jawabi, jami’in shirin na gidauniyar, Mista Ebere Mbaegbu, ya ce taron tattaunawar wani bangare ne na hadakar ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki na gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba a kan sauye-sauyen aikin ‘yan sanda da shari’a, gudanar da hukunce hukuncen laifuka da shari’a ta tanadar, gaskiya da rikon amana.
Mbaegbu ya bukaci aiwatar da tsarin sahhalewa fursunoni a matsayin mabudin rage cunkoso a gidajen yari da dabarun gyara masu laifi.
Ya jaddada cewa gudanar da adalci shi ne ginshikin duk wata al’umma da ta tabbatar da bin doka da oda.
Ya kara da cewa kokarin hadin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa wannan ginshikin ya kasance mai karfi da inganci.
“ Sahhalewa fursunoni wani muhimmin bangare ne na tsarin shari’ar mu, da nufin gyara masu laifi da kuma mayar da su cikin al’umma a matsayin ‘yan kasa masu bin doka da oda.
“Yana nuna ma’auni tsakanin matakan ladabtarwa da kuma buƙatar gyarawa, sanin cewa yuwuwar yin gyare-gyare da canji mai kyau yana samuwa a cikin kowane rayuwar bil’adama,” in ji shi.
Wani bangare na mahalarta taron sun nuna godiya ga wadanda suka shirya taron, inda suka ce taron ya samar musu da wani dandali mai kima da za su iya shiga tattaunawa mai mahimmanci.
Mahalarta taron sun bayyana ra’ayoyinsu tare da tantance halin da tsarin shari’a ke ciki game da sahhalewa fursunoni da kuma babban tasirinsa kan gudanar da shari’ar laifuka a Najeriya.
NAN ta ruwaito cewa mahalarta taron sun hada da kungiyoyin fararen hula, ‘yan sanda, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Kasa (NCoS), Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), masu gabatar da kara da lauyoyi, da dai sauransu.(NAN) ( www.nannews .ng )
HMH/BRM
=========
Tace wa: Bashir Rabe Mani