Najeriya na asarar dala biliyan 10 a duk shekara sakamakon asarar bayan girbi – Kyari  

 

Bayan girbi

Daga Aisha Ahmed 

07030065142

Kangire, (Jigawa), Satumba 16, 2025 (NAN) Ministan Noma da Samar da Abinci, Sen. Abubakar Kyari, ya ce Najeriya na asarar dala biliyan 10 a duk shekara sakamakon asarar da ake yi bayan girbi.

Kyari ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da kungiyar noma da samar da ababen more rayuwa a karkara (GRAIN) Pulse Center a kauyen Kangire, na karamar hukumar Birnin-Kudu, Jigawa.

Ya ce ana tafka asara ne sakamakon rashin wajen ajiya, rashin ababen more rayuwa, karancin kayan sarrafawa, dumamar yanayi, ambaliyar ruwa, gurbacewar kasa, da karuwar ruwan sama a fadin kasar.

A cewarsa, noma na bayar da kusan kashi 24 cikin 100 na GDPn Najeriya, inda kananan manoma ke noma kusan kashi 70 cikin 100 na abincin kasar.

“Ta hanyar karfafa wa kananan manoma da kayan aiki na zamani, fasaha, da kasuwanni, za mu iya zakulo cikakkiyar arzikin ƙasarmu da mutanenmu,” in ji Ministan.

 Kyari ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, na baiwa harkar noma fifiko a matsayin ginshikin kawo sauyi ga al’ummar kasar, yana mai jaddada cewa an mayar da hangen nesa zuwa aikace.

Ya bayyana yadda tsare-tsaren kamfanoni masu zaman kansu ke da muhimmancin gaske wajen karfafa tsarin abinci a Najeriya da kuma karfafa juriya kan asarar da ake yi bayan girbi.

Ministan ya ce, cibiyar pulse zata yi aiki ne a matsayin hadaddiyar cibiyar noma, samar da ababen more rayuwa, da raya karkara, ta yadda za ta hada dukkan sassan aikin gona waje guda.

Ya kara da cewa, cibiyar da aka tanadar na da kayan aiki na zamani, za ta samar da yanayi mai aminci na fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, kuma za a yi irin ta a fadin kasar baki daya.

Har ila yau, Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Tuggar, ya jaddada karfin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, wajen ci gaba.

Ya kuma yaba da yadda aka samar da irin wadannan cibiyoyi a cikin al’ummomin noma na Jigawa.

“Wannan yunkuri zai amfanar da Najeriya saboda fa’idodi da yawa, musamman haɗa kayan aiki da fasaha na zamani,” in ji Tuggar.

Ya yabawa shugaba Tinubu da gwamnan Jigawa ta Umar Namadi, kan yadda suka ba da fifiko wajen samar da abinci a cikin manufofin ci gaban su.

Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da yadda Jigawa ta karbi bakuncin cibiyar na farko a kasar, inda ya bayyana ta a matsayin wata kyakkyawar fasaha domin dorewar rayuwar karkara.

Ya ce aikin zai zaburar da tattalin arziki, tare da nuna sauye-sauyen da al’umma za su samu ta hanyar bunkasa noma.

Namadi ya bayyana cewa, wurin ya hada da tsarin hadaka mai amfani da hasken rana, cibiyoyin sadarwa na zamani, da kuma hidimomin da suka kunshi dukkan sassan darajar aikin gona.

Ya nanata kudirin gwamnatinsa na karfafa aikin gona domin samar da ayyukan yi, fadada ababen more rayuwa, da inganta rayuwa.

Shugaban Karamar Hukumar Birnin-Kudu, Mista Muhammad Uba, ya yi alkawarin ba da goyon baya ga ajandar Shugaba Tinubu, inda ya bayyana yadda jihar Jigawa ta ba da fifiko a fannin noma da samar da abinci.

Ya kara da cewa Gwamna Namadi ya dauki muhimman matakai domin kawo sauyi da kuma daidaita harkar noma a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kyari ya kaddamar da cibiyar GRAIN Pulse Centre a Kangire, a wani bangare na shirin sabunta bege. (NAN) (www.nannews.ng)

AAA/KTO

 

======

Fassarar Aisha Ahmed

Jihar Kaduna ta fadada hanyoyin karkara domin bunkasa noma

 

Hanya

 

By Mustapha Yauri

 

Zaria (Jihar Kaduna) Satumba 8, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Kaduna ta fara aikin gina titunan karkara a fadin jihar domin bunkasa harkokin noma a jihar.

Yunkurin dai na nufin saukaka zirga-zirgar kayan amfanin gona, tare da inganta kasuwannin manoma da kuma karfafuwar samar da abinci a fadin jihar.

Babban sakataren ma’aikatar noma, Alhaji Umar Abba ne, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Zariya, cewa, shirin na da nufin rage asarar da ake samu bayan girbi.

Ya ce, gwamnatin Gwamna Uba Sani, ta jajirce wajen samar da hanyoyin shiga karkara, domin karfafa ayyukan noma da bunkasa zamantakewa da tattalin arziki, tare da ci gaban al’umma baki daya.

Abba ya kara da cewa, shirin na hadin gwiwa ne tsakanin bankin duniya da gwamnatin jihar Kaduna, a karkashin shirin samar da ayyukan noma na karkara (RAAMP).

Babban sakataren ya ci gaba da cewa, a kwanakin baya ma’aikatar ta gudanar da ziyarar gani da ido, a kashi na biyu na wasu al’ummomin da suka ci gajiyar ayyukan hanyoyin.

Sakataren ya bukaci ‘yan kwangila, da su kammala ayyukan cikin gaggawa tare da kiyaye ka’idoji.

Hakazalika, Ko’odinetan ayyukan, Malam Zubairu Abubakar, ya zayyana wasu daga cikin ayyukan hanyoyin da ake gudanarwa a matakai daban-daban.

Ya ce sun hada da tituna Sama da kilomita 50 na Fala zuwa Sayasaya, Masama Gadas zuwa Anchau Road a karamar hukumar Ikara.

Sauran in ji shi, sun hada da titin Gora zuwa Kwoi, mai tsawon kilomita 3.5 a karamar hukumar Jaba, sannan titin Aduwan Gida zuwa Fadan Kaje mai nisan kilomita 5.6 a Zonkwa.

Akwai kuma na karamar hukumar Zangon Kataf da titin Illa zuwa Kofato, mai kilomita 13.4 a karamar hukumar Igabi da titin Sabon Tasha zuwa Juji zuwa Unguwar Barde da sauransu.

A cewar mai gudanar da aikin, duk ayyukan hanyoyin shiga karkara karkashin RAAMP, za a kammala sune a karshen shekarar 2025.

Don haka, ya yi kira ga mazauna yankin da masu amfani da hanyoyin, da su ci gaba da bada hadin kai ga ‘yan kwangilar, domin kammala da ayyukan cikin sauki da kuma dace. (NAN) (www.nannews.ng)

 

AM/KLM

Fassarar Aisha Ahmed

 

Mamakon ruwan sama yana yi mana barazana – manoman shinkafa a Abakaliki

 Douglas Okoro

Abakaliki, 6 ga Agusta, 2025 (NAN) Manoman shinkafa a Abakaliki, sun koka kan yadda ake samun mamakon ruwan sama, wanda a cewarsu yana barazana ga noman shinkafa a shekarar 2025.

Manoman, sun bayyana damuwar tasu ne a wata tattaunawa da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba a garin Abakaliki.

An dai samu mamakon ruwan sama a bana wanda ya yi sanadin ambaliya da asarar amfanin gona a manyan yankunan da ake noman shinkafa a jihar.

Mista Emmanuel Nwali, wani fitaccen manomin shinkafa a karamar hukumar Izzi, ya ce kusan rabin gonar shinkafarsa ta nutse sakamakon ruwan sama mai yawa.

“Ambaliya ta lalata yawancin gonakinmu, abin da ya rage tuni ya koma tawaya.

“Kusan kullum ana ruwan sama tun tsakiyar watan Yuli. Wataƙila ba za mu yi tsammanin samun girbi mai yawa a wannan kakar ba,” in ji Nwali.

Wani manomi, Mista Chinedu Okenwa, ya ce ya yi asarar gidajen yara na reno sakamakon ambaliyar ruwa, wanda ya yi sanadin asarar manyan albarkatu.

“Ban san yadda zan gyara asarar da aka yi ba, domin a halin yanzu, ba zan iya dasa komai ba don ya lalace.

“Muna fuskantar karancin amfanin gona a wannan kakar, kuma hakan na iya haifar da hauhawar farashin shinkafar gida a shekara mai zuwa,” in ji shi.

Hakazalika, Mista Aloysius Njoku, wani Mai nomana kasuwanci, ya ce ya yi asarar wani kaso mai yawa na gonar shinkafa sakamakon ambaliya, kuma yana fargabar ci gaban zai yi illa ga girbi.

“Damina da ambaliyar ruwa sun yi mummunar barna, idan ba a yi wani abu ba, shinkafa za ta yi karanci da tsada, kuma kowa zai ji ajikinsa,” in ji Njoku.

Misis Sylvia Elom, wata ma’aikaciyar gwamnati kuma mai noman shinkafa, ta bayyana ddamuwarta inda tace barnar da ruwan sama ya yi a gonaki ta yi kamari kuma abun zai shafi mutane da dama da suka dogara da noman shinkafa domin tafiyar da rayuwarsu.

“Shinkafa ita ce babbar hanyar samun kudin shiga ga yawancin mutanenmu wadanda galibi manoma ne, idan ambaliyar ruwa ta lalata mana gonakinmu, ba a bar mu da komai ba kenan,” in ji ta.

A halin da ake ciki, Dr Paul Onwe, wani kwararren manoma mai zaman kansa, ya bayyana cewa akwai gagarumar matsala a noman shinkafa idan damuna ta tsawaita aka samu ambaliya.

Ya kara da cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya, yana haifar da babbar barazana ga gonakin shinkafa, musamman wadanda ke cikin fadamu.

Ya shawarci manoma da su mai da hankali sosai kan hasashen yanayi kafin su fara noman shinkafa, yana mai cewa gwamnatin tarayya na bayar da gargadin a farkon kowace kakar noma.

“Filayen da ke cikin ƙasa suna fama da takurewar girma, ƙarancin abinci mai gina jiki, da cututtukan fungal,” Onwe yayi gargaɗi.

Wata majiya daga ma’aikatar noma ta jihar Ebonyi da ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar na bin diddigin illolin da ambaliyar ruwa ta haifar a gonaki a halin yanzu.

Ya kara da cewa gwamnati na kuma tattara rahotanni daga yankunan da abin ya shafa domin daukar matakan da suka dace.

NAN ta ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), a hasashenta na yanayi, ta bayyana jihar Ebonyi a matsayin daya daga cikin jihohin da ake sa ran za su fuskanci ambaliyar ruwa a lokacin damuna ta 2025.

Jihar Ebonyi dai na daya daga cikin jihohin da ake noman shinkafa a Najeriya, kuma ‘yan kasuwar shinkafa a manyan kasuwannin Abakaliki, sun bayyana fargabar cewa farashin shinkafar na iya tashi sakamakon rashin girbi da ake sa ran za a samu. (NAN) (www.nannews.ng)

 

Edited by Aisha Ahmed

Matawalle ya bada tallafin tirela 15 na takin zamani ga jam’iyyar APC ta Zamfara

Matawalle ya bada tallafin tirela 15 na takin zamani ga jam’iyyar APC ta Zamfara

Matawalle ya bada tallafin tirela 15 na takin zamani ga jam’iyyar APC ta Zamfara
Noma
Daga Ishaq Zaki
Gusau, Aug. 25, 2024 (NAN) Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya baiwa jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara tallafin tireloli 15 na takin zamani, domin karawa shirin shugaban kasa Bola Tinubu na kawo sauyi a fannin noma.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na jihar, Malam Yusuf Idris, wanda ya fitar a Gusau ranar Lahadi.
Idris ya ce Matawalle ya mika wa jam’iyyar tallafin ne ta hannun shugaban jam’iyyar APC na jiha Alhaji Tukur Danfulani.
Ya ce sakataren jam’iyyar na jiha Ibrahim Umar-Dangaladima ne ya karbi rabon takin a madadin jam’iyyar.
Idris ya ce, “Karimcin da Matawalle ya yi wa jam’iyyar APC a jihar na da nufin bunkasa ayyukan noma da bunkasar tattalin arziki da ci gaba.
“Motocin takin zamani guda 15 na rabon takin ne ga wadanda suka amfana a fadin jihar kuma hakan na daga cikin shirin na shugaba Tinubu na kawo sauyi a harkar noma.
“Wannan ya yi dai-dai da shirye-shiryen noma da Gwamnatin Tarayya ta yi na tabbatar da an samu noma mai yawa a daminar noman da ake yi a yanzu.”
Ya bayyana cewa za a raba kayayyakin ne kyauta a fadin jihar.
A halin da ake ciki, Danfulani ya kuma godewa ministan, wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar a jihar, ya kuma yaba da irin goyon bayan da yake baiwa ‘ya’yan jam’iyyar a jihar.
Shugaban hukumar ya bada tabbacin cewa takin zai kai ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar a daukacin unguwanni 147 na kananan hukumomi 14 na jihar.
“Wadanda za su ci gajiyar wannan karimcin za su hada da mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar na jiha, shugabannin jam’iyyar daga kananan hukumomi da kuma gundumomi.
“Sauran wadanda suka amfana sun hada da dattawan jam’iyyar, matasa, da sauran masu ruwa da tsaki a fadin jihar,” in ji shi.
Shugaban ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyar a jihar bisa hakuri da goyon bayan da suka ba jam’iyyar, wanda hakan ke karawa jam’iyyar farin jini da karbuwa a tsakanin al’ummar jihar.
Ya bukace su da su kasance masu bin doka da oda, su kuma ci gaba da marawa gwamnatin Tinubu baya da addu’a a kasar nan.(NAN)( www.nannews.ng )
IZ/OJI/BRM
============
Tace wa: Maureen Ojinaka/Bashir Rabe Mani

Manoman chitta sun yi asarar biliyan N12 a 2023 – cewar Minista 

 

 

Manoman chitta sun yi asarar biliyan N12 a 2023 – cewar Minista

 

Asara

 

Daga Doris Esa

 

Abuja, Aug. 22, 2024 (NAN) Gwamnatin Tarayyan Najeriya tace manoman chitta a kasar sun yi asarar kudi kimanin biliyan N12 a sanadiyar annobar chutar chitta da ta afkawa gonaki a 2023.

 

Sanata Aliyu Abdullahi, karamin Ministan, a ma’aikatar Gona, da Tattalin Abinci, ya sanar da hakan yayin kaddamar da taron ba da hora wa masu horar wa, wanda hukumar inshora ta gona ta shirya a ranar Alhamis a Abuja.

 

Ministan ya haska kadan daga cikin matsalolin da manoman suka fuskanta a yayin noman damina na 2023, inda manoman chitta a JIhar Kaduna suka yi asara mai matukar yawa sanadiyar annobar chutar chittan.

 

Abdullahi yace manoman sun rasa kimanin kashi 90 daga cikin dari na amfanin gonarsu a noman da suka yi a daminar bara.

 

“Kadan daga cikin manoman chittan  da suka yiwa gonakin su garkuwan inshora ne suka  karbi diyya na daga asarar da suka yi sanadiyar annobar chutar chittan.

 

“Wa dannan jerin manoman za su yi alfaharin komawa gona ba tare da wani tallafin kudi dan kadan ba, kuma ba kamar yan uwansu manoman da basu yiwa gonakinsu garkuwan inshora ba, wadanda a yanzu sai sun kwashe duk abun dake cikin asusun su, dan komawar su zuwa gona.

 

“Wannan shine darasin da yazama dole akanmu; kamar yadda make a dukkan lokuta mukan samu kanmu a cikin asara sanadiyar zuwan mummunar damuna daya ko biyu, wannan be shafi karancin abinci ba,” a cewar sa.

 

Abdullahi yace alkalumman hashashe na ambaliyar ruwan sama na 2024 wanda maikatar ruwa da tsaftace muhalli ta fitar, ta hankaltar da kananan hukumomi 148 a jihohi 31 ha suke cikin barazanar ambaliyar ruwan sama a yankunan su.

 

Ya ci gaba da cewa rahotonni na watanin farkon shekara da ake ciki sunyi nuni da cewa kananan hukumomi 249 a jahohi 36 tare da birnin tarayya sun shigo cikin jerin yankuna da suke da saukin samun hadarin ambaliyar.

 

“A sauka ke, kananan hukumomi 397 daga cikin 774 a Najeriya, ko kuma kashi 51 daga cikin wajajen noma a kasar na cikin hadarin samun ambaliyar ruwan sama,” a cewar sa.

 

“Hakika muna sheda wa a bayyane a yanzu ba a wani lokaciba babbar barazanar dumamar yanayi da illar da ke tare da ita a tattare da amfanin gonakinmu na gida a tsarikanmu na kasa baki daya,” a bayanin da ya kara,” ministan ya fada.

 

Abdullahi yace tsare-tsaren na gaba gaba, na maikatar gwamnatin tarayya tare da hadinkan kamfanoni masu zaman kansu, da kuma hukumar NAIC da ta PULA, wanda sune mashawartan  kamfanin inshoran gona wanda suke gudanar da tsare tsaran National Agricultural Growth Scheme Agro-Pocket (NAGS-AP).

 

Ya kuma kara da cewa ya tabbata cewa dumamar yanayi gaskiyace ta tabbata dolene a shigar da tsarin inshora cikin harkar noma a matsayin ta ta abokiyar tafiya a cikin tsarin gwamnatin ta NASG dan tabbatar da dorewa da kuma masu buƙatar wadatar abinci sosai a kasa.

 

Ministan yace tsarin NAGS-AP wanda ya fara a 2023 yayin noman rani na alkama ya haifar da amfanin gona mai yawa. (NAN) (www.nannews.ng)

 

ORD/JPE

 

=======

 

Edita Joseph Edeh

Fassara daga Abdullahi Mohammed/Bashir Rabe Mani