Kungiyar IPMAN za ta dabbaka ingancin man fetur a fanfunan gidajen mai
IPMAN
Daga Stanley Nwanosike
Enugu, 25 ga Agusta, 2025 (NAN) Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ta ce tana shirin dabbaka ingancin famfun mai a gidajen mai, ta hanyar magance magudi da kuma munanan ayyuka.
Shugaban kungiyar IPMAN reshen Jihar Enugu, Cif Chinedu Anyaso, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Enugu, jim kadan bayan kammala babban taron kungiyar(AGM), na shekarar 2025.
Sashen Enugu na IPMAN, ya kunshi masu sayar da man fetur masu zaman kansu a jihohin Enugu, Anambra da Ebonyi, da kuma wasu sassan jihohin Abia, Imo, Kogi da Cross River.
Anyaso, ya ce mambobin kungiyar, sun amince gaba daya a taron AGM, kan a tabbatar da ingancin famfunan mai, domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ci moriyar kudadensu.
Ya jaddada cewa, IPMAN ta himmatu wajen daukaka martabarta wajen hidima da ingancin kayayyaki, inda ya kara da cewa: “IPMAN ta kuduri aniyar kafa wata rundunar da za ta tabbatar da bin dukkanin mambobinta.
“Wannan ya zama dole ne domin ingantaccen aikin samar da wutar lantarki.”
A cewarsa, za a kaddamar da kwamitin ne a watan Satumba mai zuwa, kuma za a gudanar da ayyukan ne ta hanyar kwazo a kowace jiha dake karkashin wannan runduna.
“Domin a tsaftace tsarin da kuma tabbatar da cewa an kiyaye martabar kungiyar IPMAN da gidajen man ‘ya’yanmu, mambobin kungiyar a lokacin taron kungiyar, sun amince da cewa dole ne a dakatar da magudi da kuma munanan ayyuka.
“IPMAN za ta kafa wani kwamiti na aiki na yau da kullun nan ba da jimawa ba, yayin da mambobin kungiyar baki daya suka amince da a ci tarar kudi mai yawa, tare da sanya takunkumi ga duk wani gidan mai da ya gaza mallakar kowane memba,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa, kungiyar ta kuduri aniyar yin tsayin daka wajen tunkarar matsalar, ta hanyar ladabtarwar cikin gida; kamar yadda kungiyar ta kawar da gurbataccen man fetur.
Shugaban kungiyar, ya bayyana cewa, kungiyar IPMAN Enugu, ta kuma yaba da irin nasarorin da gwamnoni da gwamnatocin jihohi daban-daban suke yi kan ayyukan raya kasa musamman hanyoyin mota da na tsaro a jihohin yankin.
“Mun samu kwarin guiwa da jajircewar gwamnonin, wajen ci gaba da samar da ingantaccen yanayin kasuwanci da kuma samar da titina na kayayyakin man fetur, don isa ga kowane lungu da sako na sashin,” in ji shi.
Anyaso, ya tabbatar da cewa mambobin kungiyar sun amince baki daya cewa za su sake rubutawa Gwamna Chukwuma Soludo na Anambra takarda, kan batun IGR na gidajen mai a Anambra.
“Mun yaba masa kan tattaunawar da aka yi zuwa yanzu; duk da haka, muna kira ga duk masu ruwa da tsaki, da su zo kan teburin tattaunawa, don warware sabanin da ke tsakaninsu, su yi sulhu cikin lumana domin amfanar kowa da kowa,” in ji shi.
Shugaban ya ce, mambobin kungiyar sun kuma yanke shawarar sake rubutawa Gwamna Soludo takarda kan bashin sama da Naira miliyan 900 da ake bin mambobin kungiyar IPMAN da suka samar da dizal don gudanar da fitilun tituna a jihar.
“Gwamnatin Jihar Anambra ta ci basuka tun shekara daya da ta wuce, duk da wasiku da kiraye-kirayen kai-tsaye har sau uku ga Gwamna da Jami’an Jihar da abin ya shafa, har ya zuwa yanzu ba a yi komai ba.
“Muna bin hanyar diflomasiyya tunda ba ma son mu umurci mambobinmu da su shiga yajin aiki ko kuma su daina sayar da albarkatun man fetur, domin hakan zai kara sanya talakawa a wahala da kuncin rayuwa.
“Idan ‘yan kungiyar IPMAN suka tafi yajin aiki, a bayyane yake cewa litar man fetur na iya haura kusan N2,000 zuwa N3,000 a jihar, baya ga sauran illolin da wannan yunkuri zai haifar.
“Duk da haka, muna son gwamnatin jihar ta saurari kokenmu da kuma halin da ‘yan kungiyarta IPMAN ke ciki, wadanda suka samar da kayayyaki kuma a halin yanzu suna bin cibiyoyin kudi.”
Anyaso ya jaddada cewa, a cikin ‘yan watanni ‘yan kungiyar IPMAN din guda takwas a Anambra, wadanda suke bin gwamnatin jihar bashi sun mutu sakamakon damuwa da kaduwa, domin matsin lamba da hukumomin kudi ke yi, na neman a biya su lamuni mai tsanani.
“Wasu daga cikin cibiyoyin hada-hadar kudi sun karbe tashoshinsu, wasu kuma tuni aka rufe wasu da dama kuma sun kori ma’aikatansu saboda gazawar kudi,” inji shi.
Shugaban ya kara da cewa, mambobin sun kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi walwala, ingantattun hanyoyin da za a bi wajen daga man fetur da yadda za a yi shirin sayar da kayayyaki.
Kamar yadda ya fada, yace za a fito da shiri don isar da kayayyakin Dangote kai tsaye da kuma shirin samar da man fetur da iskar Gas na JEZCO don taimakawa mambobin.
A taron, an gabatar da jawabai daga hukumar harajin cikin gida ta tarayya, kan shigar da harajin lantarki, da kuma ta TradeGrid Limited kan yadda za a saukaka ayyukan sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a gidajen mai, da dai sauran batutuwa. (NAN) ( www.nannews.ng )
KSN/KO
Fassarar Aisha Ahmed