Shafin Labarai

Damfara : ‘Yansanda sun gargadi yan Nageria akan kutse a shafukkan yanar gizo

Damfara : ‘Yansanda sun gargadi yan Nageria akan kutse a shafukkan yanar gizo

Gargadi

Damaturu, Satumba 25, 2024 (NAN) Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta gargadi mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan da wasu mutane masu gayyatar tattaunawar karya a shafukkan zumunta na yanar gizo don gudin damfara.

DSP Dungus Abdulkarim, Kakakin rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Laraba.

Ya ce wata kungiya ce ta kikiri taron don yin anfani da shi wajen yaudaran jama’a da yi musu zamba cikin aminci.

“Masu satar bayanan jama’a sun kirkiri tarurrukan intanet na karya kuma suna aika sakonnin gayyata ta hanyar yanar gizo ga jama’a.

“Da zarar mutum ya danna hanyar haɗin yanar gizon, sai su yi masa kutse a asusun ajiyar sa na banki da sauran bayanan sirri,” in ji shi.

Kakakin ya ce a wasu lokutan, yan damfaran na fakewa da cewa su maikatan banki ne masu inganta asusun abokan cinikinsu.

” Sukan aika da lambar kalmar sirri ta OTP zuwa kafofin sada zumunta ko kuma wayar hannu, kuma su bukaceku da ku mayar da lambar sirrin don yin rijista ko kuma tabbatar da asusunku.

“Duk wanda ya yi haka, yana baiwa ‘yan damfarar damar cire kudi daga asusunsa cikin mintuna kadan,” in ji shi.

Jami’in ya kuma bukaci jama’a da su yi hattara da masu aikata laifuffukan yanar gizo tare da kaucewa bada bayyanan banki ga duk wanda bai cancanta ba.

Ya shawarci abokan huldar bankin da su tabbatar da irin wadannan bukatu ta hanyar kiran waya ko ziyartar bankunan su ko cibiyoyin hada-hadar kudi don karin bayan.

“Kada ka taɓa aika lambobin OTP ko mahimman bayanai zuwa wuraren da ba a tantance ba. Yi hattara da tarukan yanar gizo ko sabunta asusunka.

“Ku sa ido akan asusunku akai-akai kuma ku kai rahoton duk wani abun da ba daidai ba ga jamian tsaro,” in ji shi.

A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Garba Ahmed, ya gargadi masu laifin da su daina aikata hakan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani. (NAN) (www.nannews.ng)

NB/RSA

======

Rabiu Sani-Ali ya gyara

Mutane sun bar gidajensu don ambaliyar ruwa da ta lalata garuruwa 10 a Kebbi – NEMA

Mutane sun bar gidajensu don ambaliyar ruwa da ta lalata garuruwa 10 a Kebbi – NEMA

Ambaliyar ruwa

Daga Ibrahim Bello
Shanga (Jihar Kebbi), Satumba 25, 2024 (NAN) Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta ce al’ummomi goma ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a karamar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi.
Mista Aliyu Shehu-Kafindagi, shugaban  hukumar NEMA a Sokoto ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagar hadin guiwa zuwa yankunan da abin ya shafa a ranar Laraba.
Ya kara da cewa lamarin ya bar mutane akalla 2,000 da suka rasa matsugunansu, wadanda ba su da wani zabi da ya wuce guduwa zuwa wasu wuraren.
“Al’amarin da ya faru a tsakanin 17 zuwa 22 ga watan Satumba, a sakamakon ruwan sama mai yawa ne da kuma samun karin ruwa daga kogin Neja, lamarin da ya sa wasu ginegine suka nutse. 
“ Garuruwa 10 da abin ya shafa a karamar hukumar Shanga, sun hada da, Kunda, Dala- Maidawa, Dala-Tudu, Dala-Mairuwa, Ishe-Mairuwa, Kwarkusa, Kurmudi, Tugar Maigani, Tukur Cika, Uguwar Gwada, Uguwar Wakili da Gundu, ” in ji shi.
A cewarsa, mutanen da suka rasa matsugunansu, galibi masunta ne, wadanda suka yi hasarar kadada mai yawa na gonaki.
Ya ce dukkanin amfanin gonakinsu iri-iri da suka hada da shinkafa, masara, gero, wake, da masara da dai sauransu sun nutse a cikin ruwa.
Shugaban hukumar ta NEMA ya kuma bayyana cewa, a yayin da tawagar ta gudanar da tantancewar, ta gano sansanin ‘yan gudun hijira da ke makarantar firamare ta Tudun Faila, inda sama da mutane 300 suka samu mafaka.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa, an gudanar da atisayen tantancewar hadin gwiwa da hukumar NEMA ta yi ne tare da hadin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA, da jami’an karamar hukumar Shanga, da kuma jami’an tsaro a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
IBI/KLM
======
Muhammad Lawal ne ya gyara

Al’ummar Katsina sun yi tir da ayyukan ‘yan Bola-jari

Al’ummar Katsina sun yi tir da ayyukan ‘yan Bola-jari

Masu fashi
Zubairu Idris
Katsina, Satumba 24, 2024 (NAN) Wasu mazauna jihar Katsina sun yi tir da ayyukan masu aikin Bola-Jari da ke lalata dukiyoyin jama’a don kwashe sandunan karfe da igiyoyin wutar lantarki.
Mazauna garin sun bayyana haka ne a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Katsina.
Sun yi nuni da cewa da misalin karfe 6:00 na safe ne irin wadannan ‘yan Bola-jarin ke fitowa daga wannan wuri zuwa wani wuri suna neman karafa, sandar karfe, roba, igiyoyi masu sulke da wutar lantarki, da kuma kayayyakin aluminum.
Mazauna yankin sun kara nuna damuwarsu kan yadda kananan yara da suka isa makaranta na daga cikin wadanda ke yawo a kan tituna domin neman wadannan kayayyaki a dukkan sassan jihar.
Dr. Habibu Kamilu, daya daga cikin mazauna yankin, ya koka kan yadda yara kanana ke shiga gidajen mutane suna satar irin wadannan karafa domin a sayar wa dillalai ko wakilansu masu sarrafa kayan.
Ya ce: “Wani lokaci waɗannan yaran ma suna tsalle-tsalle cikin gine-ginen da ba a kammala su ba don lalata linta da satar sandunan ƙarafa. 
“Abin takaici ne yadda hatta Masallatai ba su tsira daga barnar da irin wadannan mutane ke yi ba.
“Suna shiga gidaje ne domin satar tukwanen karfe da aluminum, makulli, da duk wani nau’in karafa da ya zo hanyarsu, kuma ana zarginsu da sayar da su ga dillalan karafa don samun kudi.”
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta daukar matakan dakile yaduwar wannan dabi’un tare da hana irin wadannan kananan yara yin sata tun suna kanana.
Kamilu ya kuma bukaci masu sayar da kayan shara da su tsaftace kasuwancinsu “ta hanyar kin kayan kananan yara, mutanen da ke kokwanton halsyensu kuma a daina siyan wadannan kayan da dare.”
Wani mazaunin Garin Katsina, Muhammad Abdullahi, ya koka da yadda irin wa ‘yannan matagari ke lalata tashoshi da sauran kadarorin jama’a domin neman igiyoyi da sandun karafa da kayan aluminium.
Abdullahi ya bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta daukar matakan da za su magance matsalar.
Kabir Umar, wani mazaunin yankin, ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya kuma jaddada bukatar gwamnati ta bullo da wasu matakai na kawar da wannan matsalar.
Ya ce matsalar na zama wani lamari da ke damun gidaje musamman da ma al’umma gaba daya.
Don haka ya bukaci gwamnati da ta kara kaimi wajen shirya horar da matasa domin samar da ayyukan yi ta hanyar koyar da sana’o’in hannu domin dogaro da kai. (NAN) ( www.nannews.ng )
ZI/KLM
=====
Muhammad Lawal ne ya gyara

Kotu ta dakatarda jam’iyyun siyasa 19 kawo cikasga zaben kananan hukimomin Kano

Kotu ta dakatarda jam’iyyun siyasa 19 kawo cikasga zaben kananan hukimomin Kano

Zabe
By Ramatu Garba
Kano, Sept.24, 2024(NAN) Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Talata, ta hana jam’iyyun siyasa 19 daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), ta hannun Lauyanta Rilwanu Umar, ta shigar da kara a ranar 20 ga Satumba.
Kotun da ta hana wadanda ake kara kawo cikas ga harkokin zabe a kananan hukumomi 44 (LGAs).

Wadanda ake kara sun hada da Accord Party, Action Alliance, Action Democratic Party, African Democratic Congress, All Progressives Congress, Allied Peoples Movement, All Progressive Grand Alliance, Boot Party da Labour Party.

Sauran sun hada da National Rescue Movement, New Nigeria Peoples Party, Peoples Democratic Party, Peoples Redemption Party, Social Democratic Party, Young Progressive Party, Young Party da Zenith Labour Party.
Mai shari’a Sunusi Ado-Ma’aji, ya bayar da umarnin wucin gadi da ya haramta wa wadanda ake kara yin duk wani mataki da zai hana mai shigar da kara daga gudanar da aikinsa na shari’a.

Ado-Ma’aji ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 10 ga watan Oktoba domin sauraron karar.(NAN)(www.nannews.ng)
RG/SH

=======
Sadiya Hamza ta gyara

Wike ya yi alkawarin sake dubawa, inganta Babban Tsarin Abuja

Wike ya yi alkawarin sake dubawa, inganta Babban Tsarin Abuja

Bita

By Philip Yatai

Abuja, Satumba 24, 2024 (NAN) Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Mista Nyesom Wike, ya jaddada kudirin gwamnatin babban birnin tarayya na sake duba da kuma inganta tsarin babban birnin tarayya Abuja.

Wike ya bayyana haka ne a lokacin da wata tawagar hukumar hadin gwiwa ta kasar Japan (JICA) ta kai masa ziyara a Abuja ranar Talata.

Ya ce za a gudanar da aikin ne a karkashin wani shiri na nazari da inganta hadaddiyar tsarin raya birane na Abuja, tare da hadin gwiwar JICA.

“A gare mu, mu tabbatar da cewa aiki ne da muka kuduri aniyar aiwatar da shi, kuma za mu yi duk mai yiwuwa don ganin aikin ya samu nasara,” inji shi.

Ministan ya yi wa tawagar JICA alkawarin cewa duk abin da ake bukata daga FCTA na aiwatar da aikin za a yi shi nan gaba kadan.

Ya kuma ba wa JICA tabbacin samun hadin gwiwa mai karfi don ci gaban babban birnin tarayya Abuja, ciki har da garuruwan kewayen Abuja. 

Shi ma da yake jawabi, Mista Shehu Ahmad, Sakataren zartarwa na Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA), ya ce sake duba tsarin babban birnin tarayya Abuja na da matukar muhimmanci domin tunkarar kalubalen da ake fuskanta a babban birnin tarayya.

“Muna magana ne game da tallafawa wurare ta fuskar samar da ababen more rayuwa, samar da ruwa, samar da wutar lantarki, da Kuma magudanar ruwa.

“Muna kuma duba bukatar samar da birni mai kyau, ta yadda birnin zai kasance daya daga cikin manyan biranen duniya.

” Cigaban birni ya kasance kalubale, kuma muna jin cewa yakamata su duba wadancan wuraren don inganta shi,” in ji shi.

Ahmad ya ce karuwar al’umma a Abuja ya haifar da bukatar duba samar da ayyukan yi.

Ya ce kungiyar ta JICA tare da goyon bayan wata tawagar kwararru daga sassa masu muhimmanci na FCTA da FCDA sun fara tattara muhimman bayanai don tsara rahoton fara aikin.

A cewarsa, za a kira taron kasa da kasa domin neman bayanai daga masu ruwa da tsaki da zarar an amince da rahoton fara aiki.

Tun da farko, Mista Matsunaga Kazuyoshi, jakadan kasar Japan mai cikakken iko a Najeriya, ya ce ayyukan cigaba, abinci mai gina jiki da kuma ayyukan raya birane kadan ne daga cikin dimbin ayyukan da kungiyar JICA ke aiwatarwa a babban birnin tarayya.

Kazuyoshi musamman ya ce Hada Ƙarfi don Inganta Abinci a FCT da kuma kawar da ayyukan bahaya a fili ya sami gagarumar nasara.

Ya nemi ƙarin haɗin gwiwa tare da FCTA don zurfafa aikin da ya dace don yin tasiri ga ƙarin al’ummomin FCT.

Da yake magana kan bita da kuma inganta tsarin babban birnin tarayya Abuja, Mista Nobukuyi Kobe, Sashen Kula da Kayayyakin JICA, ya ce manufar ita ce tabbatar da dorewar daidai da manufofin gwamnati.

Kobe ya ce, aikin farko shi ne samar da dabarun raya ababen more rayuwa na yanki ga Babban Birnin Tarayya da garuruwan da ke kewayen Abuja, da kuma hadaddiyar tsare-tsaren raya birane daga shekarar 2025 zuwa 2050.

Ya kara da cewa kashi na biyu shine  ingantacciyar damar tsarawa da jami’an aiwatar da shirin da aka duba.

Ya ce, duk da haka, ana sa ran FCTA za ta ba da goyon baya wajen hanzarta aika wasiku da ma’aikatar harkokin waje.

Har ila yau, FCTA, in ji shi, ana sa ran za ta amince da shirin da aka yi nazari da kuma sabunta shi, tare da dokar tsara birane da yanki, da kuma haɗin gwiwar FCTA da FCDA. (NAN) ( www.nannews.ng )

FDY/ RSA

=====

Rabiu Sani-Ali ya gyara

Majalisar Kasa ta amince da gina tituna 14 a jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa

Majalisar Kasa ta amince da gina tituna 14 a jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa

Tituna

By Salif Atojoko

Abuja, Satumba 23, 2024 (NAN) Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da gina tituna da gadoji 14, wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, a jihohin Ekiti, Adamawa, Kebbi da Enugu.

Ministan ayyuka David Unahi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron FEC.

Ya ce sauran suna jihohin Cross River, Ondo, Osun, Ebonyi, Abia da kuma Imo.

Ya ce an bayar da hanyoyin ne, baya ga kwangilar gyara da gyaran gadar Gamboru da ke kan titin Gamboru-Ngala/Kala-Balge a cikin jihar Borno.

Ministan ya ce FEC ta kuma amince da sabuwar kwangilar gyaran hanyar Maraban-Kankara/Funtua a jihar Katsina da kuma gina titin mota mai tsawon kilomita 258, wani bangare na babbar titin Sokoto/Badagry mai lamba 1,000, Sashe na 2, Phase 2A.

Hakazalika, ya ce FEC ta amince da kwangilar gine-gine tare da hada hanyar Afikpo-Uturu-Okigwe  a jihohin Ebonyi, Abia da Imo (Sashe na 2).

Ya ce haka ma FEC ta amince da kwangilar hanyar Bodo-Bonny a Rivers, wanda Julius Berger zai aiwatar.

“FEC ta amince da karin Naira biliyan 80 don kammala wannan aikin, wanda ya kawo jimillar kudin zuwa Naira biliyan 280.

“Na gaba shine gadar Mainland ta Uku, wanda aka kashe a karkashin aikin gaggawa,” in ji shi.

Ya ce a lokacin da gwamnati mai ci ta hau karagar mulki, gadar nan ta Third Mainland ta zama abin tsoro.

“Tsarin yana da bambancin shimfidar ƙafa ɗaya; wanda ya haifar da hatsari da yawa, kuma akwai matattun kaya a gadar Mainland ta Uku.

“Don haka, an yi haka kuma har zuwa Falamo da Queens Drive. Ya zo da hasken rana, kyamarori na CCTV da tashoshi na agaji, don kawar da toshe hanyoyin,” inji shi.

Ya bayyana cewa duba dukkan ayyukan.

“Kada ku manta cewa kudin farko na ayyukan ya kai Naira biliyan 155 kuma gwamnatin da ta shude ta sake duba shi zuwa Naira biliyan 797.

“Berger ta dage cewa kudin kwangilar da aka duba ya kamata ya kai Naira tiriliyan 1.5. Ba mu da wannan kudin kuma Ministan Tattalin Arziki da ni da kaina na bi ta hanyar kuma muka yi ganawar sirri da Berger,” in ji Umahi.

Ya ce daga karshe ya nemi amincewar shugaban kasa ya raba ayyukan zuwa uku domin a yi kashi biyu kan bashin haraji, sannan Julius Berger ya yi daya.

“Don haka sashin farko yana da kilomita 38, ba a kawo shi Majalisar ba. Za a yi shi da kankare.

“Kashi na biyu shi ne Berger za ta yi shi ne kilomita 82, cikin kashi na biyu, kuma za a yi da kwalta za su yi ta aiki da shi sannan kashi na uku shi ne, kilomita 17 kawai za a yi da siminti.” Yace.

Ya ce FEC ta amince da na Julius Berger a kan jimillar kwangilar Naira biliyan 740. Sai dai ya ce sauran biyun ba a gabatar da su ba domin amincewa.

“Idan ka cire kusan Naira biliyan 400 da gwamnatin baya ta biya, to abin da ya rage kusan Naira biliyan 340 ne. Abin da kudin kwangilar tafiyar kilomita 164 ke nan kuma abin da FEC ta amince da shi kenan a yau,” in ji Umahi.

Ministan ya ce hukumar ta FEC ta amince da aikin titin Lekki Deep Seaport.

A karshe ya ce ya gano cewa sama da motocin man fetur 3,000 ne suka yi jerin gwano domin daukar man a matatar Dangote duk an ajiye su ne a sabuwar hanyar da aka gina a bakin tekun Lekki zuwa Calabar.

“A fasaha, ba a taɓa gina hanyoyin don ɗaukar nauyi ba, don haka yana da tasiri mai yawa,” in ji shi.

Ya ce FEC ta amince da cewa ya kamata a ba wa gwamnatin tarayya fili a yankin, domin samun masu rangwamen su gina wurare. 

Umahi ya ce “Gidan shakatawa ne da za a biya kudin shiga, ta yadda dukkan manyan motoci za su iya ajiye su a can cikin aminci kuma shimfidar ya sha bamban da na titin,” in ji Umahi. (NAN) (www.nannews.ng)
SA/SH

=====
Sadiya Hamza ta gyara

Gwamnatin Amurka ta agazawa  wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Gwamnatin Amurka ta agazawa  wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills

 

Gwamnatin Amurka ta agazawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri


Taimako

Da Mark Longyen

Abuja, Sept.23, 2024(NAN)Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin jin kai ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri da sauran wurare.

“Amurka ta yi matukar bakin ciki da mumunar ambaliyar ruwan da ta addabi Maiduguri da sauran sassan jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka, da barnata dukiya, da kuma rabuwar iyalai da dama.  

“Muna mika ta’aziyyarmu ga wadanda abin ya shafa, iyalansu, da duk wadanda wannan bala’in ya shafa.

“A martanin da hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke bayarwa mun bayar da taimako ga wadanda abin ya shafa ta hanyar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da abokan aikinmu,” in ji ofishin jakadancin Amurka a Abuja ranar Litinin.

“Ta hanyar shirin samar da abinci ta duniya (WFP), USAID na samar da abinci ga sansanoni hudu da ke karbar ‘yan gudun hijirar kuma ya kai sama da mutane 67,000 a ‘yan kwanakin da suka gabata.  

“WFP kuma tana ba da agajin abinci na gaggawa ga mata masu juna biyu da masu shayarwa, ciki har da yara ‘yan kasa da shekaru biyar,” in ji ta.

Ofishin jakadancin ya ci gaba da cewa, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa (IOM) tana amfani da dala miliyan 3 na farko na tallafin da hukumar USAID ta bayar domin magance matsalolin ambaliyar ruwa a fadin kasar.  

Ta ce hukumar ta USAID tana kuma tallafawa hukumar kula da jiragen sama ta Majalisar Dinkin Duniya UNHAS wajen gudanar da jigilar kayan abinci zuwa yankunan da ba sa isa a cikin garin Borno da Maiduguri domin magance bukatun gaggawa.

 “Sauran abokan huldar USAID da suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa da na cikin gida suna sake dawo da kudaden da ake da su don ba da taimako ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri da kuma karamar hukumar Jere da ke makwabtaka da su.

 “Mun yaba da jarumtaka da juriyar mutanen Maiduguri da kuma namijin kokarin da masu bayar da agaji na farko, da ma’aikatan agaji, da hukumomin kananan hukumomi ke yi a kasa wajen gudanar da muhimman ayyuka.

“Tunaninmu ya kasance tare da mutanen Borno a wannan lokaci mai wuya,” in ji ofishin jakadancin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa bala’in ya kai ga asarar rayuka, da barnata dukiya, da kuma raba iyalai da dama, lamarin da ya janyo ambaliyar ruwa da agajin jin kai.


NAN ta ruwaito cewa hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta ce sama da mutane 30 ne suka mutu sannan sama da 400,000 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri.

A ranar 9 ga watan Satumba, dubban mazauna garin sun tsere daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye yankunan Fori, Galtimari, Gwange, da Bulabulin a Maiduguri.

Ambaliyar ruwan ta afku ne sakamakon rugujewar madatsar ruwa ta Alau da ta yi gaba daya.

Gwamnatin Borno ta bude sansanin ‘yan gudun hijira (IDP) ga wadanda abin ya shafa a fadin jihar…(NAN)(www.nannews.ng)
YEN/SH

=======
Sadiya Hamza ta gyara

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

 

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

Ficewa

Daga Franca Ofili

Abuja, Satumba 23, 2024 (NAN) Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.

Aliyu Dawobe, jami’in hulda da jama’a na ICRC ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce kungiyar ta kuma bayar da gudummawar jakankuna 150 ga hukumar NRCS, da asibitin kwararru na jihar da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar.

“ Madatsar ruwan Alau ta fashe ne da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Satumba, abinda ya haddasa ambaliyar ruwa a Maiduguri.

“Kafin faruwar lamarin, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye yankuna da dama a jihar lamarin da ya shafi hanyoyin shiga.

“Fiye da mutane 414,000 ne abin ya shafa tare da lalata gidaje da dama da amfanin gona.

“Akwai matukar damuwa ga fararan hula wadanda rikicin yankin ke cigaba da shafa,” in ji Dawobe.

A cewarsa, hadakar kungiyoyin agaji na ICRC da na NRCS ne ya shiga aikin bincike da ceton.

Ya ce sun kuma gudanar da aikin kwashe marasa lafiya tare da bayar da agajin gaggawa, da kuma hada kan iyalai da ambaliyar ruwa ta raba su da kuma kula da gawarwaki cikin aminci.

“Kungiyoyin sun kwaso gawarwaki 22 zuwa yau, yayin da yara 76 suka koma ga iyalansu.

“An kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ruwan ya shafa.

“Hukumar ICRC ta kuma ba da gudummawar jakunkuna 150 ga NRCS, Asibitin Kwararru na Jiha da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA).

“NRCS ta kaddamar da ayyukan inganta tsafta a sansanoni uku da su ka karbi bakuncin al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa tare da hadin gwiwar ICRC,” in ji Dawobe.

Dawobe ya ce a wani bangare na shirin rigakafin cutar kwalara, ICRC ta tanaji magunguna da suka hada AquaTabs da hodar chlorine don shirin ko ta kwana.

“Ana horar da masu aikin sa kai na NRCS kan yadda ake amfani da wadannan kayan kuma suna ba da fifiko wajen tsaftace rijiyoyi, famfunan hannu, rijiyoyin burtsatse, da sauran hanyoyin ruwa na al’umma.

“ICRC ta shirya zaman tallafi na zamantakewa don ma’aikatan NRCS da masu sa kai waɗanda suka shiga cikin ayyukan mayar da martani da yawa.

“A cikin kwanaki masu zuwa, ICRC tare da haɗin gwiwa tare da NRCS, za ta mika muhimman kayan gida ga gidajen da abin ya shafa, ciki har da taburmai, barguna, kayan dafa abinci, gidajen sauro, bokiti, sabulu, kayan tsaftacewa da tufafi, ” Yace.

A cewarsa, ICRC ta kuma taimaka wa Nijar, Kamaru da Chadi don magance matsalar ambaliyar ruwa.(NAN)( www.nannews.ng)

FNO/AMM

Fassara daga Nabilu Balarabe

=======

 

Tinubu ya yi maraba da nasarar da APC ta samu a zaben gwamnan Edo

Tinubu ya yi maraba da nasarar da APC ta samu a zaben gwamnan Edo

Nasara

By Salif Atojoko

Abuja, Satumba 23, 2024 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Sanata Monday Okpebholo, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar, murnar nasarar da ya samu a zaben.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da ya doke sauran wadanda ke neman kujerar.

Tinubu ya yabawa shugabannin jam’iyyar APC na kasa da shugabannin Edo da gwamnonin jam’iyyar da suka yi aiki tukuru domin samun nasara, in ji Mista Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru a cikin wata sanarwa.

Shugaban ya ce nasarar ta shaida irin goyon bayan da jama’a ke ba jam’iyya mai mulki, da manufofin ci gaba, da shirin farfado da tattalin arziki da kuma jajircewa wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya roki Okpebholo da kada ya yi murna da nasarar da ya samu amma ya gan ta a matsayin kira ga hidima.

Ya kara masa kwarin guiwa da ya nuna kwarjini ta hanyar tuntubar abokan hamayyarsa na siyasa da hada kan mutanen Edo don tabbatar da ci gaba.

Tinubu ya kuma yabawa sauran ’yan takarar da suka halarci zaben bisa gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da dimokuradiyyar Najeriya gaba, inda ya ce fafatawar siyasa cikin lumana irin ta ranar Asabar tana bayyana Najeriya a matsayin turbar dimokradiyya.

Shugaban ya bukaci duk wadanda sakamakon zaben ya fusata da su nemi hakkinsu ta hanyar doka.

Bugu da kari, shugaban ya yabawa al’ummar Edo kan yadda suka gudanar da zabe cikin tsari da lumana a lokacin zaben, inda ya nuna amsuwar tsarin dimokuradiyyar a kasa bayan shekaru 25.

“Ina yaba wa INEC da jami’an tsaronmu da suke aiki ba dare ba rana domin gudanar da atisayen cikin nasara, cikin lumana da kuma rashin cikas.

Tinubu ya kara da cewa “INEC ta sake nuna cewa ta himmatu wajen shirya zabe mai inganci a kasarmu.” (NAN) (www.nannews.ng)

SA/HA

Hadiza Mohammed-Aliyu ta gyara

Ambaliyar: Gwamnatin Borno ta kafa kwamitin rabon agaji

Ambaliyar: Gwamnatin Borno ta kafa kwamitin rabon agaji

Kwamitin

Daga Yakubu Uba
Maiduguri, Satumba 23, 2024 (NAN) Gwamna Babagana Zulum na Borno ya kafa kwamitin mutane 32 kan rabon agajin bala’in ambaliyar ruwa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga sakataren gwamnatin Borno, Alhaji Bukar Tijjani.

Gwamnatin ta ce kwamitin na da Alhaji Baba Gujubawu, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan sa ido da ayyuka a matsayin Shugaba, yayin da Farfesa Ibrahim Umara na jami’ar Maiduguri a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran mambobin sun hada da wakilan hukumar raya arewa maso gabas, ‘yan sanda, EFCC, ICPC, DSS, NSCDC, NEMA, SEMA, sarakunan addini da na gargajiya da kuma ma’aikatu da ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa (MDAs).

Wakilan kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya a Borno da kungiyoyin farar hula (CSOs) suma za su kasance mambobi. 

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, ambaliyar ruwan da aka yi a ranar 10 ga watan da ya wuce sakamakon rugujewar madatsar ruwan Alau, ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata dukiyoyi da har yanzu ba a tantance adadinsu ba a cikin garin Maiduguri da kewaye. (NAN)

YMU/SH

======

edita Sadiya Hamza