An tsaurara matakan tsaro yayin da aka fara zaben Kananan hukumomi a jihar Ondo
An tsaurara matakan tsaro yayin da aka fara zaben Kananan hukumomi a jihar Ondo
Tsaro
Akure, Janairu 18, 2025 (NAN) An fara zaben kananan hukumomi a jihar Ondo, a ranar Asabar tare kulawar dimbin jami’an tsaro a fadin jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an lura da jami’an ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence (NSCDC) a rumfunan zabe da wurare masu mahimmanci.
Da misalin karfe 7:00 na safe an ga jami’an tsaro a muhimman wurare a kan manyan tituna a fadin jihar, ciki har da gaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ondo, da kuma kan titin filin jirgin sama a karamar hukumar Akure ta Arewa.
Hakazalika a cikin zagayen Agbogbo, mahadar Fiwasaye/Mobil da kuma gaban A Division, ‘yan sandan Najeriya, a kan titin Oba Adesida, an ga tawagar jami’an tsaro suna aiwatar da dokar hana zirga-zirga yayin da suke mayar da ababen hawa da mutanen da ba sa gudanar da muhimman ayyuka. .
A Okitipupa da kewaye, an kuma ga jami’an tsaro a manyan tituna da kuma wasu rumfunan zabe.
Sai dai NAN ta ruwaito cewa wasu mazauna yankin suna gudanar da sana’o’insu yayin da aka ga wasu matasa a filin Estate na Ijapo suna wasan kwallon kafa da kuma a Unguwar Ward 10 dake Odo-Ikoyi a karamar hukumar Akure ta Kudu.
An kuma lura da harkokin kasuwanci a wasu yankunan jihar na gudana, yayin da wasu masu shaguna da masu sayar da abinci suka bude domin kasuwanci. (NAN)
(www.nannews.ng)
Reporters/AOS
==============
Bayo Sekoni ya gyara