An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka
An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka
Rantsuwa
Washington, Janairu 20, 2025 (dpa/NAN) An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurika a zagayen ginin Capitol na Amurka da ke Washington.
Trump ya yi rantsuwar ne a wani gagarumin biki da ya samu halartar iyalansa, da tsaffin shugabannin Amurka da wasu manyan baki daga Amurka da kasashen waje.
“Lokacin kyakkyawa na Amurka ya fara a yanzu,” in ji shi a cikin jawabinsa na farko.
“Zan sanya Amurka a gaba,” in ji Trump. (dpa/NAN) (www.nan news.ng)
YEE
====
(Edited by Emmanuel Yashim)