An gudanar da zaben cike gurbi cikin lumana a jihar Jigawa
Zabe
Daga Muhammad Nasir Bashir
Babura (Jigawa), Aug. 16, 2025 (NAN) An gudanar da zabe cikin lumana a zaben cike gurbi na mazabar Babura-Garki a Jigawa a ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun da karfe 8:00 na safe, masu kada kuri’a suka yi dafifi zuwa rumfunan zabe, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke da isasshen tsaro a fadin yankin.
Jami’an ‘yan sandan Najeriya (NPF), jami’an tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) da sauran su, sun tabbatar da kiyaye doka da oda a rumfunan zabe da sauran muhimman wurare a Babura da Garki.
A rumfar zabe ta Garki Kofar Fada (003) da firamaren Yamma (005) a garin Garki, an ga jami’an zabe suna shirya kayan zaben tun kafin a fara da karfe 8:30 na safe.
Mista Ibrahim Shehu, jami’in zabe na 1 a rumfar zabe, ya ce sun yi isassun shirye-shirye domin saukaka gudanar da aikin.
Wani sashe na masu kada kuri’a sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda suka jin dadi ga yadda jami’an tsaro suka gudanar da aikinsu.
Zaben ya samu fitowar jama’a da dama da suka hada da ministan tsaro, Badaru Abubakar, da karamar Ministan Ilimi Hajiya Suwaiba Ahmad.
An kuma ga wasu mazauna yankin suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum, yayin kada kuri’a cikin lumana a mafi yawan wuraren da aka ziyarta. (NAN) (www.nannews.ng)
MNB/ISHO/ RSA
Fassara Aisha Ahmed