Ambaliyar ruwar Maiduguri: Sama da tallafin N12b aka samar ga wadanda abin ya shafa 

Ambaliyar ruwar Maiduguri: Sama da tallafin N12b aka samar ga wadanda abin ya shafa 

Spread the love

Ambaliyar ruwar Maiduguri: Sama da tallafin N12b aka samar ga wadanda abin ya shafa 

Taimako 

By Yakubu Uba 

Maiduguri, Satumba 19, 2024 (NAN) Gwamnatin Borno ta ce ta samu tsabar kudi Naira Biliyan Goma shabiyu, (N12b), da kuma kayan tallafi ga wadanda bala’in ambaliyar Ruwan Alau Dam ya shafa a Maiduguri. 

Abdurrahman Bundi, Babban mai ba gwamnan Borno shawara na musamman kan kafafen yada labarai na zamani, ya bayar da karin haske game da gudummawar da aka bayar na asusun tallafawa al’ummar Maiduguri a ranar Alhamis a Maiduguri.

Bundi ya ce tallafin ya fito ne daga kamfanoni, gwamnatocin jihohi, ‘yan majalisar jiha da na kasa, daidaikun mutane, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Jerin sunayen masu ba da tallafi sun nuna cewa Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) ta ba da gudummawar N3b da kayan abinci, Aliko Dangote N2b, Aminu Dantata N1.5b, da Mohammed Indimi N1b.

Sauran wadanda suka bayar da tallafi sun hada da kananan hukumomin Borno; N1.2b, Oluremi Tinubu; N500m, jihohin Bauchi da Niger; N250m kowanne yayin da mutanen Kudancin Borno suka bayar da N200m.

Dahiru Mangal, Atiku Abubakar, Rep. Mukhtar Betara, Ali Modu Sheriff, Majalisar Wakilai, Abdulsalam Kachala, da JAIZ Bank Jihohin da suka hada da Kebbi, Yobe, Kano, Taraba, Katsina, Kaduna da Zamfara sun bada Naira 100 kowanne.

Darakta Janar na Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Buba Marwa da Matrix Energy sun ba da gudummawar tireloli 10 na taki da kayan abinci da darajarsu ta haura N120m kowanne.

Wadanda suka bada N50m sun hada da jihar Adamawa, Mr Peter Obi, Rabiu kwakwanso, Ahmed Lawan, Mohammad Maifata, Ibrahim Umar, Mohammad Imam, Ali Dalori, APC shiyyar Bauchi, Sen. Tahir Monguno, da Sen. Kaka Shehu and I8th Engineering Company. yayin da Majalisar Jihar ta bayar da gudummawar N60m.

Gwamnatin Nasarawa ta kuma ba da kyautar manyan motoci guda shida na shinkafa, spaghetti da sukari. 

Wasu mutane da dama sun ba da gudummawar tsakanin N1m zuwa N30m bi da bi. (NAN)

YMU/MNA 

Maureen Atuonwu ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *