Ambaliyar Ruwan Maiduguri: Tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta isa Borno
Ambaliyar Ruwan Maiduguri: Tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta isa Borno
Ziyarci
By Yakubu Uba
Maiduguri, Satumba 15, 2024 (NAN) Tawagar da ta kunshi kungiyoyi daban-daban a karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta isa Maiduguri a ziyarar tantance bala’in ambaliyar ruwa ta Alau Dam.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa tawagar wadda ta kunshi kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa na karkashin jagorancin babban jami’in jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Fall, sun isa Maiduguri a ranar Asabar.
Tawagar wacce ta ziyarci sansanonin domin yin mu’amala da wadanda abin ya shafa, sun kuma kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamna Babagana Zulum, inda daga bisani suka yi mu’amala da manema labarai.
Da yake jawabi, Fall ya tabbatar wa gwamnati da al’ummar Borno goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wajen tinkarar kalubalen.
“Dukkanmu muna tare da ku cikin tausayawa da hadin kai kuma za mu yi aiki tare.
“Ina so in gaya muku cewa ba za mu yi amfani da albarkatu na su yawa wajen tunkarar tallafi.
“Za mu sake mayar da hankalin kan abunda da aka tsara don ganin yadda za inganta wannan aikin kawo dauki,” in ji Fall.
Ya ce hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) za ta yi wani cikakken nazari kan bala’in da ya afku, duba da kafa shirin bada tallafi.
Da yake mayar da martani, Gwamna Zulum, ya gode wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya bisa jerin ayyukan da ta ke yi a jihar, yayin da ya kuma ba da tabbacin gwamnati na yin hadin gwiwa da su.
Zulum, wanda ya yi magana kan girman barnar da ambaliyar ta yi, ya bukaci hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da su fara mayar da hankali kan bukatun gaggawa na wadanda abin ya shafa kamar abinci, lafiya, matsuguni, tsaftar ruwa da tsafta.
“Muna bukatar mu fara fitar da wadanda abun ya shafa nan da nan na wuraren da aka gano suna da aminci don kariya daga barkewar cuta tare da shirya su don mutane su koma gidajensu.”
Ya ce akwai bukatar a tallafa wa wasu da ke amfani da makarantu a matsayin sansanin kwana domin su koma gidajensu cikin kankanin lokaci domin baiwa yara damar komawa makaranta.
“Yaranmu sun dade suna fama da rashin ilimi saboda tashe-tashen hankula kuma ba za mu iya samun damar tsallake wannan zaman gaba daya ba.”
Gwamnan ya ce tare da goyon bayan amintattun abokan aikin, gwamnatin sa ba za ta bari afkuwar ambaliyar ta hana ta aiwatar da shirinta na ci gaba ba.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa sama da mutane 414,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon mummunar ambaliyar da ta afku a Maiduguri a ranar Talata.
Shugabar yada labarai na ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA) Abuja, Ann Weru ce ta bayyana kokarin tallafin.
Weru ya ce hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta tattara bayanan a ranar 11 ga watan Satumba.
“Bayanan NEMA kuma sun nuna cewa mutane 37 sun mutu, kuma kusan mutane 58 sun samu raunuka,” in ji ta.
Ta kara da cewa damar zuwa asibitoci da makarantu da kasuwanni an samu cikas.
“An dauki adadin lalacewar abubuwan more rayuwa, gami da gadoji.
“Ana ci gaba da kwashe mutanen da ke yankunan da ke da hadari zuwa wurare mafi aminci, a cikin damuwa game da hadarin barkewar cututtuka,” in ji ta. (NAN) (www.nannews.ng)
YMU/SH/
===========
Sadiya Hamza ta gyara