Ambaliyar ruwa: Shettima ya ziyarci Maiduguri, ya ba da tirela 50 na shinkafa
Ambaliyar ruwa: Shettima ya ziyarci Maiduguri, ya ba da tirela 50 na shinkafa
Shettima
By Yakubu Uba
Maiduguri, Satumba 10, 2024 (NAN) Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ziyarci Maiduguri a ranar Talata domin jajanta wa al’ummar Borno kan bala’in ambaliyar ruwa ta Alau da ta raba dubban mutane da gidajensu.
Kashim, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa birnin da ke fama da rikici, ya samu tarba daga Gwamna Babagana Zulum, inda ya kai shi fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi, wanda shi ma ambaliyar ruwa ta afkawa.
Daga fadar, mataimakin shugaban kasar ya tuka mota zuwa sansanin Bakassi inda dubban mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu ke samun mafaka.
Shettima ya shaida wa wadanda abin ya rutsa da su cewa gwamnati za ta tallafa musu da tirela 50 na shinkafa.
Ya kara da cewa gwamnati za ta kuma hada kai da hukumar raya yankin arewa maso gabas da sauran hukumomi don ganin ba su shafe sama da makonni biyu a sansanin ba.
NAN ta ruwaito cewa a ranar Talata mazauna Maiduguri sun farka da mummunar ambaliyar ruwa da ta lakume gine-gine da dama tare da kwashe tituna da gadoji.(NAN)
YMU/ETS
=======