Ambaliyar ruwa: Badaru ya baiwa gwamnatin Jigawa tallafin N20m

Ambaliyar ruwa: Badaru ya baiwa gwamnatin Jigawa tallafin N20m

Spread the love

Ambaliyar ruwaDaga Deborah Coker

Abuja, Agusta 25, 2024 (NAN) Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 20 ga gwamnatin Jigawa domin tallafa wa ayyukan agaji na jihar ga mutanen da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa.

Badaru ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jigawa domin jajanta masa kan ambaliyar ruwa da ta addabi jihar tare da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Henshaw Ogubike, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

A cewar Ogbuike, a yayin ziyarar Badaru ya nuna alhininsa game da mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadin lalata gonaki a fadin jihar.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin tarayya na taimaka wa jihar a wannan lokaci mai cike da kalubale, yayin da ya bayyana cewa bayar da tallafin nasa ne na nuna goyon baya da kuma tausaya wa jihar.

Badaru ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa bada gudunmowar da ya yi na magance matsalar ambaliyar ruwa.

“Aikin gaggawar da kuka yi wajen bayar da agaji ga wadanda ambaliyar ta shafa abin yabawa ne,” in ji shi.(NAN)(www.nannews.ng)

DCO/KAE
======

Tace wa: Kadiri Abdulrahman


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *