Al’ummar Adamawa sun koka da barkewar bakuwar cuta
Daga Ibrahim Kado
Fufore (Adamawa), Satumba 5, 2025 (NAN) Mazauna garin Malabo a karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa, sun nuna damuwarsu kan barkewar wata bakuwar cuta da ke damun sassan jiki tare da haifar da radadi mai tsanani.
Wasu majinyata da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Malabo a ranar Juma’a, sun ce cutar kan fara ne kamar borin jiki, daga baya kuma sai ta watsu, kuma a hankali tana cin naman jiki tare da lalata kasusuwa.
Misis Phibi Sabo, ta ce ta shafe makonni tana fama da cutar.
“Abun ya fara kamar borin jiki mai zafi, daga baya ya kumbura ya fashe, sa’an nan ya fara cinye naman da ke kafada, yana lalata kasusuwa kuma ya jawo mun ciwo mai tsanani.
“Hakan ya sa ni rauni a fili, ba zan iya bayyana abin da ke faruwa da ni ba, duk da cewa na ziyarci asibiti kuma na sami magunguna,” in ji Sabo.
Ta yi kira ga gwamnati da tallafa, inda ta nuna cewa da yawa daga cikin majinyata ba za su iya yin ayyukansu na yau da kullum ko kuma tallafa wa iyalansu ba.
“Don Allah, muna son taimakon gwamnati kafin al’ummarmu ta salwanta,” Sabo ya yi kuka.
Ta kuma jaddada bukatar gwamnati ta binciki musabbabin cutar, tare da samar da kayan agaji ga gidajen da lamarin ya shafa.
Wani da abin ya shafa, Malam Junaidu Adamu, shi ma ya ce ya shafe sama da watanni biyu yana fama da irin wannan ciwon, ya bayyana irin wadannan alamomin.
“Kimanin watanni biyu da suka wuce bayan na dawo daga gona, sai na ji zafi a kafata, sai ta fara kamar borin jiki, sai ta fashe ta bazu har namana ya fara rubewa.
“Ina kashe kimanin Naira 25,000 a mako-mako wajen sayen magunguna, amma idan na sha, sai ya kara tsananta yanayin.
“Yanzu matata tana gida don ta kula da ni da yaran, wanda hakan ya shafi rayuwarmu,” in ji shi.
Adamu, ya kuma roki gwamnati da ta gaggauta kawo dauki kafin cutar ta yadu zuwa ga sauran al’umma.
Da yake tabbatar da lamarin, Hakimin Malabo, Alhaji Aliyu Hammawa, ya ce akalla mutane 30 ne abin ya shafa.
Ya ce a halin yanzu mutane takwas daga ciki suna karbar magani a asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (MAUTH) a Yola, yayin da wasu kuma ke samun kulawa a cibiyar kula da lafiyar al’umma.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar, bisa gaggauta daukar matakin da yi, tare da yin kira da a gaggauta gudanar da bincike don gano musabbabin cutar.
Shima da yake tabbatar da bullar cutar, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Adamawa, Dakta Suleiman Bashir, ya ce hukumar tare da hadin gwiwar karamar hukuma, ta dauki nauyin mutane 28 da suka kamu da cutar.
Ya tabbatar da cewa mutane takwas ne kawai suka karbi magani.
Dakta ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta riga ta biya kudin jinyar wasu a MAUTH, yayin da aka dauki samfuri domin yin gwaji.
“Ana sa ran sakamako a cikin kwanaki 10 masu zuwa. Muna kira ga wadanda abin ya shafa, da su karbi magani maimakon dogaro da magungunan gargajiya,” in ji shi.
Bashir ya bukaci mazauna yankin, da su gaggauta kai rahoton yanayin duk wani rashin lafiya da ba a saba gani ba, zuwa ga cibiyoyin kiwon lafiya don tantancewa da kyau (NAN) IMK/TIM/YMU
Edited by Yakubu Uba
Fassarar Aisha Ahmed