Almajirai 17 sun mutu acikin wata gobara a makarantar jihar Zamfara
Almajirai 17 sun mutu acikin wata gobara a makarantar jihar Zamfara
Gobara
Daga Ishaq Zaki
Gusau, Fabrairu 5, 2025 (NAN) Wata gobara ta yi sanadiyar salwantar da rayukan Almajiri goma sha bakwai a garin Kaura Namoda dake karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.
Shugaban karamar hukumar Kaura Namoda, Alhaji Mannir Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin ga
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Gusau ranar Laraba.
Haidar ya ce lamarin ya faru ne a makarantar kur’ani ta Malam Aliyu Na Malam Muhammadu Ghali a
daren ranar Talata.
Yace `’ gobarar ta dauki tsawon sa’o’i da dama kuma ta yi sanadiyar rayukan yara Almajirai 17 yayin da wasu 17 da abin ya shafa suka jikkata.”
A cewar Haidar, an yi jana’izar dukkan almajiran a garin Kaura Namoda a ranar Laraba.
Ya kara da cewa “mun ba da umarnin ba da kulawar gaggawa ga yara 17 da suka jikkata, wadanda a halin yanzu
ke karbar magani a asibiti.
“Mun kafa wani kwamiti da zai binciki musabbabin barkewar wutar da kuma irin barnar da aka yi.”
Haidar ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa yaran da suka rasu, ya jikan su da Aljannah, ya kuma baiwa iyalansu
hakurin jure wannan babban rashi. (NAN)(www.nannews.ng)
IZ/OIF/JPE
=========
Ifeyinwa Okonkwo/Joseph Edeh ne suka gyara