Al-Habibiyyah ta yi kira da a fitar da zakka yadda ya kamata domin magance talauci
Al-Habibiyyah ta yi kira da a fitar da zakka yadda ya kamata domin magance talauci
Zakka
By Muhydeen Jimoh
Abuja, Feb. 10, 2025 (NAN) Babban limamin kungiyar Al-Habibiyyah Islamic Society (AIS) na kasa, Sheik Fuad Adeyemi, ya yi kira da a fitar da zakka yadda ya kamata domin samun sauƙin rayuwa tsakanin Musulmai.
Zakka ta wajaba ga musulmin da suka cancanta, tana bukatar su biya wani kashi na dukiyoyinsu a duk shekara idan ta zarce wani adadi.
Wannan aikin addini yana inganta haɗin kai ta hanyar raba dukiya ga talakawa.
Adeyemi ya yi wannan kiran ne a lokacin bukin ranar Zakka ta Kasa karo na 4 da Rarraba Zakkar ga Jama’a karo na 14 na Kungiyar Al-Habibiyah Islamic Society Zakka/Edowment Foundation.
Taron wanda aka gudanar a unguwar Paduma da ke Abuja, ya shaida yadda aka raba tsabar kudi naira miliyan 15, da tallafin karatu, da sauran kayayyakin karfafawa mutane 90 da suka ci gajiyar tallafin.
A wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, Limamin ya bayyana cewa an raba kudaden ne da nufin rage radadin talauci a tsakanin Musulmi da kuma karfafa tattalin arzikin kasar.
Ya kuma yi kira ga wadanda su ka karba da su sanya kudi da kayan cikin hikima, ta yadda su kuma za su ba da gudummawarsu wajen fitar da zakka a nan gaba.
“Kada talauci ya kasance a Musulunci; kawai dai mutane da yawa ba sa fitar da zakkarsu kamar yadda Allah ya umarce su.
“Wannan ne ya sa muka shirya wannan lacca domin wayar da kan al’ummar musulmi kan hanyar da ta dace ta ba da zakka da kuma muhimmancin bayar da kyauta a Musulunci,” in ji Imam.
Adeyemi ya jaddada cewa an fitar da zakka ne a bayyane, tare da tantance wadanda suka amfana da kyau kamar yadda Alkur’ani mai girma ya gindaya.
“Mun tabbatar da cewa duk wadanda suka ci gajiyar shirin sun cika sharuddan, kuma babu wani dangi na kwamitin zakka da ya ci gajiyar wannan rabon,” in ji shi.
NAN ta ruwaito cewa taron mai taken, “Bincike Waqf (Endowment) don Dorewa Matakan yaki da Talauci,” na nuna mahimmancin tallafi don tallafawa kokarin kawar da talauci na dogon lokaci. (NAN) ( www.nannews.ng )
MUYI/AMM
========
Abiemwense Moru ne ya gyara