Skip to content

Search news

Type to search stories, topics and pages.

Latest
Uncategorized

Chambas: Tawayen Abzinawa, rikicin manoma da makiyaya su ke haifar da rashin tsaro a Sahel

By 1 min read

Chambas: Tawayen Abzinawa, rikicin manoma da makiyaya su ke haifar da rashin tsaro a Sahel

Sahel
By Ginika Okoye
Abuja, Oktoba 3, 2024 (NAN) Tawayen Abzinawa da rikicin manoma da makiyaya ne ke haifar da rashin tsaro a yankin Sahel, Dr Mohamed Chambas, babban mai shiga tsakani na kungiyar Tarayyar Afirka kan Sudan, ya ce.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake gabatar da kasida a taron lacca na shekara-shekara na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
Tawayen Abzinawa a shekara ta 2012 shi ne farkon yakin Mali, daga watan Janairu zuwa Afrilun 2012, yakin da ‘yan tawaye suka yi da gwamnatin Mali da nufin samun ‘yancin kai ga yankin arewacin Mali da aka fi sani da Azawad.
Taken lacca shine “Rashin Tsaro a Sahel (2008-2024), Rarraba Kalubalen Najeriya-Farawa, Tasiri da Zabuka”. (NAN)
GINI/SH
=======

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *