Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta umurci Minista da hafsoshin tsaro su koma Sokoto
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta umurci Minista da hafsoshin tsaro su koma Sokoto
Ta’addanci
Daga Deborah Coker
Abuja, Satumba 1, 2024 (NAN) Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta umurci karamin ministan tsaro, Dr Bello Matawalle da sauran hafsoshin soja da su koma jihar Sokoto domin kawar da yankin Arewa maso Yamma daga barazanar ‘yan fashi, garkuwa da mutane da ta’addanci.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Henshaw Ogubike, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro ya fitar.
Umurnin, inji gwamnatin, wani bangare ne na kara kaimi wajen kawar da yankin Arewa maso Yamma daga barazanar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma ta’addanci.
Gwamnatin tarayya ta bayyana bakin cikinta dangane da ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a jahohin da kewaye, inda ta bayyana cewa wannan dabarar da ta dauka ya nuna jajircewar gwamnati na maido da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Matawalle ya ce yayin da suke yankin Arewa maso Yamma, za su sa ido kan yadda a ke gudanar da ayyuka tare da tabbatar da an fatattaki Bello Turji da ’yan fashin sa.
“Wadannan ’yan fashin sun rika yada bidiyon wata mota kirar sulke ta sojojin Najeriya da ta makale a wani wuri mai cike da ruwa.
“Kuma da daddare a ka bukaci jami’an da su janye don gudun kada ‘yan bindiga su yi musu kwanton bauna, daga baya cikin dare ‘yan fashin suka je wurin da ruwan tabo ya rike , inda suka dauki hoton motar sulke da ta makale suna murna.
“Wannan lamari ya faru ne a kwashabawa, karamar hukumar Zurmi a Zamfara.
“Wannan ba abu ne da za a amince da shi ba, kasancewar shugaban kasa Bola Tinubu yana bayar da gagarumin goyon baya ga rundunar sojojin Nijeriya.
“Gwamnatin tarayya ta damu matuka game da barazanar ‘yan bindiga da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma musamman.
“Don haka a shirye muke mu tura duk wasu kayan da su ka dace kuma suka wajaba don tabbatar da cewa an kawar da wadannan miyagu da kuma samar da zaman lafiya a cikin al’ummominmu,” in ji Matawalle.
Ya kara da cewa akwai bukatar a gaggauta yaki da ‘yan ta’addan domin baiwa mutane damar tafiya cikin walwala.
“Lokaci ya kure wa wadannan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda saboda karuwar ayyukan da a ke yi za su raunana dukkanin sansanonin su.
“Na yi imanin kasancewar jami’ai a yankin Arewa maso Yamma zai sa sojojinmu su kara karfi,” in ji shi.
Matawalle ya kuma tabbatar wa al’ummar jihohin Sakkwato da Katsina da Zamfara da Kebbi da ma daukacin yankin Arewa maso Yamma cewa jami’an tsaro ba za su fatattaki ‘yan bindigar ga.
“Zan kasance a yankin Arewa maso Yamma tare da jami’an CDS da sauran hafsoshin soji, tare da jagorantar jaruman mu maza da mata sanye da kayan aiki.
“Ina kuma kira ga mazauna wadannan Jihohin da su yi taka-tsan-tsan tare da ba jami’an tsaron hadin kai kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya baki daya.
Ministan ya kara da cewa: “Tsaro da jin dadin jama’a su ne babban abin da gwamnati ta sa gaba.” (NAN) (www.nannews.ng)
DCO/SH
=====
edita Sadiya Hamza