Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 2, 517, hekta 1, 000 na gonakin noma a Gombe – SEMA

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 2, 517, hekta 1, 000 na gonakin noma a Gombe – SEMA

Spread the love

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 2, 517, hekta 1, 000 na gonakin noma a Gombe – SEMA

Lalacewa

By Peter Uwumarogie

Gombe, Aug. 31, 2024 (NAN) Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), ta ce gidaje da shaguna 2,517 su ka lalace tare da gonakin noma da su kai hekta 1,000 a wata ambaliyar ruwa da ta lakume al’ummomi 33 a jihar.

Mista Ibrahim Nalado, Mataimakin Darakta a sashen bada agaji da tsare tsare na hukumar ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Asabar a Gombe.

Nalado ya ce al’ummomin da abin ya shafa sun kasance a kananan hukumomin Dukku, Funakaye da Billiri (LGA) na jihar.

A cewarsa, wadannan yankuna sun tabu ne sakamakon mamakon ruwan sama da a ka yi tsakanin ranar 12 ga watan Agusta zuwa 22 ga watan Agusta.

Ya ce, “A karamar hukumar Dukku, al’ummomi 10 ne abin ya shafa. A karamar hukumar Funakaye, al’ummomi 20 ne abin ya shafa sannan a karamar hukumar Billiri, al’ummomi uku ne abin ya shafa”.

Nalado ya ce ambaliyar da guguwar iska ta shafi galibin gidaje da filayen noma kadan a cikin al’ummomin.

Ya ce ba a samu asarar rai ba amma yara biyu sun samu raunuka a Dukku, ciki har da dabbobi bakwai da suka tafi da su.

Dangane da illar ambaliya a gonaki, mataimakin daraktan ya ce al’ummar Hina a karamar hukumar Yamaltu/Deba ta jihar ce ta fi fama da iftila’in.

Ya ce, kasa da hekta 1, 000 na shinkafa da masara da dawa da gonakin gero sun nutse cikin ruwa.

Mataimakin daraktan ya bayyana cewa tawagarsa ta ziyarci unguwar Hina a ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta, domin tantance irin barnar da aka yi.

Nalado ya bayyana tasirin ambaliya a matsayin babbar barna duba da yawan fadin yankin da abin ya shafa.

“Manoma suna shirin girbin amfanin gonakinsu.

“Manoman sun damu sosai amma saboda abu ne na kaddara sun yarda da shi cikin kyakkyawan zato,” in ji shi.

Mataimakin daraktan ya bayyana cewa a na tattara bayanai kan adadin manoman da ambaliyar ruwan ta shafa a Hina.

Nalado ya bayyana cewa hukumarsa ta tantance yawan barnar da a ka yi, amma tana tattara rahotannin domin mikawa gwamnatin jihar da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Sai dai ya ce irin barnar da a ka yi a filayen noma a Hina, zai dauki matakin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya wajen magance matsalar.

Ya kuma yi kira ga Hukumar Raya Arewa maso Gabas da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da su tallafa wa gwamnatin Jihar a kan hakan.

Mataimakin daraktan, ya kuma yi kira ga manoma da sauran mutanen da abin ya shafa da su yi hakuri.

Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnati da sauran hukumomin gwamnati za su kawo musu dauki. (NAN) (www.nannews.ng)

 

UP/COA/OCC

=====

Edita ta Constance Athekame/Chinyere Omeire


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *