Zanga zanga ta barke bisa karin farashin man fetur a Kenya

Zanga zanga ta barke bisa karin farashin man fetur a Kenya

Spread the love

Zanga zanga

Nairobi, 19 ga Mayu, 2026 (Reuters/NAN) Zanga zanga ta barke a wasu garuruwa na Kenya ranar Litinin, saboda karin farashin man fetur, ciki har da yajin aikin sufuri na jama’a, wanda ya tilastawa matafiya tafiya da lafa zuwa wurin aiki.

Kungiyar Sufuri ta kasar, ta ce a ranar Lahadi ya kamata motocin da ke da alaƙa da ƙungiyoyin membobinta su daina aiki daga tsakar dare, don nuna rashin amincewa da hauhawar farashi, inda ‘yan sanda suka yi alƙawarin magance duk wani cikas.

Hukumar Kula da Makamashi da Man Fetur ta Kenya, ta kara farashin mai da kashi 23.5 cikin 100, bayan ta kara farashinsa da kashi 24.2 cikin 100 a watan Afrilu, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara matsin lamba kan samar da mai da iskar gas a duniya.

A safiyar Litinin, an toshe hanyoyin shiga babban birnin Nairobi ta hanyar masu sufuri da kuma gungun masu zanga-zanga da suka watse.

‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a wasu yankuna, yayin da wasu masu zanga-zanga suka kunna tayoyi don hana shiga manyan hanyoyi, lamarin da ya kara ta’azzara cunkoso da kuma barin mutane da yawa da ke tafiya a kasa.

A Mombasa, babban birnin tashar jiragen ruwa na Kenya, yajin aikin ya haifar da fargabar jinkirin da ake samu wajen samar da kayayyaki.

Ministan Kudi na kasar, John Mbadi ya shaida wa tashar talabijin ta Citizen cewa, ma’aikatun kudi da makamashi suna fatan ganawa da masu kula da sufuri na jama’a a ranar Litinin don tattauna mafita, yana mai lura da cewa an riga an tallafa wa farashin da ake da shi a yanzu.

“Kenya tana shigo da kusan dukkan kayayyakin mai daga Gabas ta Tsakiya ta hanyar yarjejeniyar gwamnati da gwamnati da masu samar da mai na yankin Gulf.

“Karin farashin mai ya ƙara yawan kuɗin sufuri da kuma ƙara farashin kayan masarufi, wanda hakan ya ƙara matsin lamba ga iyalai da ke fama da tsadar rayuwa,” Ministan yace.

Ma’aikacin hulda da jama’a, Gabriel Odhiambo, mai shekaru 24, ya ce farashin sufurinsa ya ninka sau biyu kuma farashin abinci shi ma ya tashi.

Ya ce yanzu haka, farashin tumatir guda hudu suna kan farashin shilling 60 (cent 50 na Amurka), ƙarin ya ninka sau uku.

Kenya ta ƙara farashin famfon mai na super petrol a Nairobi zuwa 214.25 na Kenya ​shillings ($1.66) a kowace lita daga 206.97, dizal zuwa 242.92 ​shillings daga 196.63 na zagayowar 15 ga Mayu zuwa 14 ga Yuni, yayin da kananzir bai canza ba a shilling 152.78. (Reuters/NAN) ( www.nannews.ng )

 

HLM/CEO/AAA

Edited by Hadiza Mohammed/Chidi Opara

 

Fassarar Aisha Ahmed 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *