Fasikanci: Hisbah ta Kebbi ta kama matar aure, wasu 5 a wani samame da ta kai otal

Fasikanci: Hisbah ta Kebbi ta kama matar aure, wasu 5 a wani samame da ta kai otal

Spread the love

Fasikanci: Hisbah a Kebbi ta kama matar aure, wasu 5 a wani samame da ta kai otal

Fasikanci

Daga Lawal Taofeek
Birnin Kebbi, 15 ga Mayu, 2026, (NAN) Jami’an Hukumar Hisbah ta Kebbi, hukumar ga ke karkashin Ma’aikatar Harkokin Addini, sun kama wata matar aure da wasu mutane biyar a wani otal bisa zargin aikata rashin da’a.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wadanda aka kama sun hada da maza uku da mata uku.

Daraktan Shari’a a hukumar, Sirajo Kamba, ya tabbatar da kamawar a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Juma’a.

Ya ce an kai harin ne sakamakon bayanan sirri da hukumar ta tattara.

“A ranar 14 ga Mayu, Hukumar Hisbah ta Kebbi ta kai hari a wani otal da ke bayan Fadar Gwamnatin jiha, inda aka samu maza uku da mata uku suna aikata ayyukan rashin da’a.

“Bayan rahotanni daga jama’a, jami’an Hisbah sun kai hari a wurin suka kama mutanen da abin ya shafa.

Daraktan ya ce, “Ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a dauki matakin da ya dace bisa ga doka da ka’idojin hukumar.”

Kamba ya kara da cewa bincike ya nuna cewa daya daga cikin matan ta yi aure.

“Wannan ya nuna bukatar karfafa tarbiyya da tsoron Allah a cikin al’umma.”

Ya bukaci iyaye da su sa ido sosai kan motsin ‘ya’yansu da ayyukansu domin hana su shiga cikin halaye da ke lalata dabi’u da mutuncin al’umma. (NAN)(www.nannews.com.ng)

LOT/KLM
=========
Muhammad Lawal ne ya gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *