Sojoji sun yi nasarar dakile yunkurin kai hari a wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano 

Sojoji sun yi nasarar dakile yunkurin kai hari a wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano 

Spread the love

Sojoji sun yi nasarar dakile yunkurin kai hari a wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano

Hare-hare
Daga Muhammad Nur Tijani
Kano, Janairu 2, 2025 (NAN) Sojojin Rundunar Hadin Gwiwa (JTF) sun yi nasarar dakile wani yunkurin kai hari da ‘yan bindiga suka yi a wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano bayan wani dogon artabu da bindiga.

Al’amarin, wanda ya fara a daren Alhamis kuma ya dauki tsawon sa’o’i da sanyin safiyar Juma’a, ya faru ne a Yankwada, Babanduhu da sauran kauyukan makwabta a yankin.

Da yake tabbatar da lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya a Kano, Maj. Zubair Babatunde, ya ce ‘yan bindigar sun yi yunkurin kai hari kan al’ummomin a kan babura yayin da suke harbi akai-akai.

Babatunde ya ce harin wani aikin ramuwar gayya ne bayan rasa wasu daga cikin mayakan ‘yan bindigar da sojoji su ka yi a lokacin wani arangama da suka yi a makon da ya gabata.

A cewarsa, maharan sun kai hari a wuraren kauyukan da abin ya shafa da misalin karfe 1:00 na safe, wanda ya haifar da martani cikin gaggawa daga sojojin.

“Sojoji sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar yadda ya kamata kuma sun kore su,” in ji shi.

Babatunde ya kara da cewa shiga tsakani na JTF kan lokaci ya hana asarar rayuka da kuma barna mai yawa ga dukiya a yankunan da abin ya shafa.

Ya tabbatar wa mazauna yankin jajircewar sojoji na kare rayuka da dukiyoyinsu, yana mai kira gare su da su ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu inganci da kuma kan lokaci.

Kakakin rundunar ya ce sojoji na nan a shirye don hana sake kai hare-hare da kuma wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.(NAN)(www.nannews.ng)

MNT/BRM
=========
Bashir Rabe Mani ne ya gyara

 

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *