Gwamnatin Sokoto da UNICEF sun samar da akwatunan shawarwari 332, teburin taimako 166

Gwamnatin Sokoto da UNICEF sun samar da akwatunan shawarwari 332, teburin taimako 166

Gwamnatin Sokoto da UNICEF sun samar da akwatunan shawarwari 332, teburin taimako 166

Spread the love

Gwamnatin Sokoto da UNICEF sun samar da akwatunan shawarwari 332, teburin taimako 166

UNICEF

Daga Habibu Harisu

Sokoto, Disamba 17, 2025 (NAN) Gwamnatin Jihar Sakkwato ta samar da akwatunan shawarwari 332 da kuma teburin taimako 166 don ƙarfafa shigar al’umma cikin aiwatar da harkokin kiwon lafiya da sauran ayyuka.

Sakataren Dindindin a Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Alhaji Bashiru Maigari, ya ce an samar da kayayyakin ne tare da haɗin gwiwar UNICEF.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Sakkwato (SSPHCDA), Dakta Bilyaminu Yari-Sifawa, da Shugaban Kwamitin Cigaban Unguwa na Jiha (WDC), Dokta Bala Gadanga ne suka gabatar da kayayyakin.

Maigari ya ce an tsara kayayyakin ne don ƙarfafa shigar al’umma, inganta hanyoyin bayar da ra’ayoyi, inganta gaskiya da riƙon amana wajen aiwatar da shirye-shirye a matakin farko.

Ya kuma ce kowanne mai lura da kwamitin yana da hakkin samun tallafin Naira 5,000 na tsawon watanni uku na farko.

Ya yaba wa UNICEF kan tallafin kuma ya sake nanata kudirin ma’aikatar na inganta dabarun sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a.

Yari-Sifawa ya kuma ce za a yi amfani da ra’ayoyin da aka tattara don magance karancin ma’aikata, da kuma daidaita munanan halayen ma’aikata wanda hakan zai inganta ayyukan kiwon lafiya.

Ya yaba wa UNICEF kan tallafin kuma ya yi alƙawarin tabbatar da aiwatar da ayyukan da ake buƙata yadda ya kamata da kuma sauran abubuwan da suka wajaba.

Shugaban WDC, wanda ya yi magana a madadin al’ummomin da suka amfana, ya kuma yi alƙawarin yin amfani da kayayyakin yadda ya kamata tare da jan hankalin al’umma don cimma nasara a aiwatar da manufofi da ayyuka. (NAN)(www.nannews.ng)

HMH/USO

An gyara ta Sam Oditah

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *